Jiya Litinin ne aka kaddamar da Cibiyar Confucius ta Dijital da Fasaha ta Jami’ar Mulungushi a Jami’ar din da ke Kabwe, a lardin Tsakiya na kasar Zambiya. An bayyana cewa, wannan ita ce cibiyar Confucius ta farko a Afirka da ta mayar da ilimin dijital da fasaha a matsayin babban jigonta, kuma za ta ba da gudummawar sabon karfi ga cudanyar kimiyya da fasaha da kuma al’adu tsakanin Sin da Afirka.
An kafa wannan cbiyar Confucius ne ta hanyar hadin gwiwar Jami’ar Watsa Labarai da Sadarwa ta Zhejiang da Jami’ar Mulungushi. Za ta yi kokarin samar da tsarin horo wanda ya hada da koyon Sinanci, fasahar kwaikwayon tunanin dan Adam da kuma ilmin watsa labarai, tare da amfani da dabaru na dijital da na fasaha wajen karfafa koyar da Sinanci a kasar, ta yadda za a samar wa matasan Sin da Zambiya dandali na musayar al’adu da fasahar dijital.
Babban sakataren ma’aikatar ilimi ta Zambiya, Dr. Kelvin Mambwe, ya bayyana a yayin bikin kaddamar da cibiyar cewa, Zambiya na ba da muhimmanci ga horar da ma’aikata a fannin fasahar dijital da hadin gwiwar ilimi na kasa da kasa, kuma yana fatan wannan Cibiyar Confucius ta Dijital da Fasaha za ta ci gaba da horar da matasa masu iya harshen Sinanci da kwarewar dijital, domin ba da gudummawa ga ci gaban tattalin arziki da zamantakewar Zambiya. (Bilkisu Xin)














