Maaikatar raya aladu da yawon shakatawa ta kasar Sin ko MCT, ta sanar a jiya Litinin cewa, kasuwar yawon bude ido ta cikin gidan kasar ta bunkasa matuka, a fannin adadin zirga-zirga da kashe kudade tsakanin watan Janairu zuwa Satumban bana, kamar dai yadda wasu alkaluman binciken balaguro a cikin kasar da maaikatar ta fitar suka nuna.
Alkaluman sun nuna cewa, cikin watannin tara na farkon shekarar nan, mutane sun yi tafiye-tafiye sama da biliyan 5.3 a cikin gida, adadin da ya karu da kaso 6.2 bisa dari a mizanin shekara-shekara. Cikin wannan adadi, zirga-zirgar alummun kasar mazauna birane ta haura biliyan hudu, adadin da ya karu da kaso 6.6 bisa dari kan na shekarar bara, yayin da adadin zirga-zirgar alummun kasar mazauna karkara ta kai biliyan 1.27, watau karuwar kaso 5.1 bisa dari a shekara.
A bangaren kashe kudade kuwa, kudaden da masu yawon bude ido na cikin gida suka kashe a waadin watannin tara, ya karu da kaso 2.2 bisa dari a mizanin shekara-shekara, inda adadin ya kai yuan tiriliyan 4.95, watau kusan dalar Amurka biliyan 737. Cikin wannan jimilla, kudaden da mazauna birane suka kashe sun kai yuan tiriliyan 4.14, karuwar da ta kai ta kaso 2.2 bisa dari, yayin da na mazauna sassan karkarar kasar ya kai yuan biliyan 810, watau karuwar kaso 2.1 bisa dari. (Mai fassara: Saminu Alhassan)













