Babban Hafsan Sojojin Ƙasa, Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya sake jaddada aniyar rundunar sojin Nijeriya na tallafa wa kamfanonin cikin gida da ke kera motocin yaƙi masu sulke da sauran kayan aikin soji.
Shaibu ya bayyana hakan ne ranar Talata yayin ziyarar aiki da ya kai ofishin kamfanin PROFORCE Group a Jihar Ogun, inda ya jaddada muhimmancin ƙarfafa masana’antun tsaro na cikin gida domin inganta aikin sojoji da tsaron ƙasa.
A cikin wata sanarwa da Mukaddashiyar Daraktar Hulɗa da Jama’a ta Sojojin Ƙasa, Kanal Appolonia Anele, ta fitar ranar Laraba, ta ce babban hafsan ya yaba wa kamfanin PROFORCE kan ƙirƙire-ƙirƙirensa da gudummawar da yake bayarwa wajen bunƙasa masana’antun tsaro na cikin gida.
Shaibu ya ce ci gaba da zuba jari wajen kera kayan aikin soji a cikin ƙasa zai rage dogaro da masu sayar da kayayyaki daga ƙasashen waje, da inganta samuwar kayan aiki, tare da ƙara wa rundunar damar tunkarar barazanar tsaro cikin sauri da inganci.
Ya ce rundunar sojin ƙasa a ƙarƙashin jagorancinsa za ta ci gaba da goyon bayan manufar Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta bunƙasa amfani da kayayyakin cikin gida da ƙarfafa masana’antun tsaro na ƙasa.
A cewarsa, samun masana’antun tsaro masu ƙarfi a cikin ƙasa yana da muhimmanci wajen tabbatar da tsaron ƙasa, musayar fasaha da bunƙasa ƙarfin aikin soji na dogon lokaci.
A nasa jawabin, Manajan Darakta kuma Babban Jami’in Gudanarwa na PROFORCE Group, Ade Ogundeyin, ya gode wa babban hafsan bisa ziyarar, tare da jaddada aniyar kamfanin na samar da ingantattun kayayyakin tsaro da za su biya buƙatun rundunar sojin ƙasa.
Ziyarar na daga cikin ƙoƙarin rundunar na ƙarfafa haɗin gwiwa da masana’antun tsaro na cikin gida domin rage dogaro da kayan aikin soji da ake shigowa da su daga ƙasashen waje, inganta musayar fasaha da kuma ƙara dogaro da kai wajen samar da kayan aikin da ake buƙata.














