ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, October 28, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

2027: Daraktan Yaƙin Neman Zaɓen NDC Ya Buƙaci Atiku Ya Marawa Tafiyar Obi-Kwankwaso Baya

by Muhammad
56 minutes ago

Daraktan Yaƙin Neman Zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC), Ibrahim Hussain Abdulkarim, ya buƙaci tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, da ya haɗa kai da Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso domin ƙarfafa haɗin kan ’yan adawa gabanin zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Abdulkarim ya yi wannan kira ne a wata hira da gidan talabijin na Arise, inda ya ce haɗin kan ’yan adawa zai ƙara musu damar samun nasara a zaɓen mai zuwa.

Ya bayyana cewa tuni Obi da Kwankwaso suka amince su yi aiki tare a ƙarƙashin NDC, yana mai cewa ƙofar jam’iyyar a buɗe take ga Atiku da sauran ’yan siyasa da ke son shiga haɗin gwiwar.

ADVERTISEMENT

A cewarsa, ba lallai ne haɗin kan ’yan adawa ya gudana ƙarƙashin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ba, domin ana iya cimma hakan a ƙarƙashin NDC.

Abdulkarim ya ce abin da suke nema shi ne sauran shugabannin ’yan adawa su haɗa kai da su domin faɗaɗa goyon bayan da suke da shi a faɗin ƙasar.

LABARAI MASU NASABA

ADC-PCC Ta Nemi Majalisa Ta Yi Fatali Da Bashin Tinubu Na Dala Biliyan 20 Da Fam Biliyan Ɗaya

Adamawa Ta Tinubu Ce – Fintiri

Ya kuma yi watsi da sukar da ake yi wa tsarin yaƙin neman zaɓen NDC, yana mai cewa bai kamata a kwatanta jam’iyyar siyasa da ƙungiyoyin magoya baya ba. Ya ce NDC na da ƙungiyoyin goyon baya sama da 1,000.

Bugu da ƙari, Abdulkarim ya yi kira ga ’yan Nijeriya da ke fargabar za a iya murɗe sakamakon zaɓe da su shiga NDC. Ya ce jam’iyyar za ta yi kamfen cikin lumana tare da ƙoƙarin tabbatar da cewa an kare ƙuri’un masu zaɓe.

NDC ta riga ta bayyana Obi a matsayin ɗan takararta na shugaban ƙasa, yayin da Kwankwaso zai tsaya takarar mataimakin shugaban ƙasa a zaɓen 2027.

Muhammad
+ postsBio
  • Muhammad
    Mutum Biyar Sun Rasa Rayukansu A Hatsarin Ayarin Motocin Gwamnan Neja A Minna
  • Muhammad
    Waɗanne Ƙalubale Waɗanda Aka Yi Garkuwa Da Su Suke Fuskanta Bayan Sun Dawo Gida?
  • Muhammad
    SERAP Ta Kai Gwamnatin Nijeriya Kotu Kan Zargin Badakalar Naira Biliyan 78.8
  • Muhammad
    Peter Obi, Marowaci Ne Ba Zai Iya Shugabancin Nijeriya Ba – Wike

MASU ALAKA

ADC-PCC Ta Nemi Majalisa Ta Yi Fatali Da Bashin Tinubu Na Dala Biliyan 20 Da Fam Biliyan Ɗaya
Siyasa

ADC-PCC Ta Nemi Majalisa Ta Yi Fatali Da Bashin Tinubu Na Dala Biliyan 20 Da Fam Biliyan Ɗaya

October 27, 2026
Adamawa Ta Tinubu Ce – Fintiri
Siyasa

Adamawa Ta Tinubu Ce – Fintiri

October 26, 2026
NDC Ta Tsige Ɗan Takararta A Borno Kan Zargin Yi Wa Atiku Kamfe
Manyan Labarai

NDC Ta Tsige Ɗan Takararta A Borno Kan Zargin Yi Wa Atiku Kamfe

October 26, 2026

LABARAI MASU NASABA

2027: Daraktan Yaƙin Neman Zaɓen NDC Ya Buƙaci Atiku Ya Marawa Tafiyar Obi-Kwankwaso Baya

2027: Daraktan Yaƙin Neman Zaɓen NDC Ya Buƙaci Atiku Ya Marawa Tafiyar Obi-Kwankwaso Baya

October 28, 2026
Mutum Biyar Sun Rasa Rayukansu A Hatsarin Ayarin Motocin Gwamnan Neja A Minna

Mutum Biyar Sun Rasa Rayukansu A Hatsarin Ayarin Motocin Gwamnan Neja A Minna

October 28, 2026
Hada-Hadar Yawon Shakatawa A Cikin Gidan Sin Ta Bunkasa Cikin Watanni Tara Na Farkon Bana

Hada-Hadar Yawon Shakatawa A Cikin Gidan Sin Ta Bunkasa Cikin Watanni Tara Na Farkon Bana

October 27, 2026
An Kaddamar D Cibiyar Confucius Ta Dijital Da Fasaha Ta Jami’ar Mulungushi A Zambiya

An Kaddamar D Cibiyar Confucius Ta Dijital Da Fasaha Ta Jami’ar Mulungushi A Zambiya

October 27, 2026
Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Biyan Tallafin Sufuri Ga Ma’aikata Naira 70,000 A Duk Wata

Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Biyan Tallafin Sufuri Ga Ma’aikata Naira 70,000 A Duk Wata

October 27, 2026
ADC-PCC Ta Nemi Majalisa Ta Yi Fatali Da Bashin Tinubu Na Dala Biliyan 20 Da Fam Biliyan Ɗaya

ADC-PCC Ta Nemi Majalisa Ta Yi Fatali Da Bashin Tinubu Na Dala Biliyan 20 Da Fam Biliyan Ɗaya

October 27, 2026
An Kaddamar Da Taron Kirkire-Kirkire Da Ci Gaba Ba Tare Da Gurbata Muhalli Ba Na Ziri Daya Da Hanya Daya A HK

An Kaddamar Da Taron Kirkire-Kirkire Da Ci Gaba Ba Tare Da Gurbata Muhalli Ba Na Ziri Daya Da Hanya Daya A HK

October 27, 2026
Kungiyar JIBWIS Ta Miƙa Ɗan Agajin Da Ake Zargi Da Kalaman Ƙiyayya Ga Ƴansanda

Kungiyar JIBWIS Ta Miƙa Ɗan Agajin Da Ake Zargi Da Kalaman Ƙiyayya Ga Ƴansanda

October 27, 2026
IRENA: Kasar Sin Ta Ba Da Gagarumar Gudummawa Wajen Sauyin Makamashi A Duniya

IRENA: Kasar Sin Ta Ba Da Gagarumar Gudummawa Wajen Sauyin Makamashi A Duniya

October 27, 2026
Atiku Ya Buƙaci Majalisar Dattawa Ta Yi Watsi Da Buƙatar Ciwo Bashin Tinubu

Atiku Ya Buƙaci Majalisar Dattawa Ta Yi Watsi Da Buƙatar Ciwo Bashin Tinubu

October 27, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.