Shugaban kasar Sin kuma babban sakataren kwamitin kolin JKS Xi Jinping, ya jaddada bukatar gaggauta gina tsarin kaifafa basira na kasar Sin a fannin ilimin falsafa da kimiyyar zamantakewa.
Xi, wanda kuma shi ne shugaban hukumar zartarwar rundunar sojojin kasar Sin, ya yi kiran ne cikin umarnin da ya bayar dangane da ingiza ci gaba mai inganci a fannin falsafa da kimiyyar zamantakewa.
Ya ce akwai matukar bukatar zurfafa binciken ilimi bisa tsari, da fayyace ma’anar sabbin ka’idojin gudanar da jam’iyyar kwaminis.
Daga nan sai ya yi kira da a gaggauta gina tsarin kasar Sin na kaifafa basira a fannin falsafa da kimiyyar zamantakewa, da gaggauta amsa tambayoyin da jama’a da lokaci da Sin da ma duniya ke gabatarwa, kana a kara azamar cimma sabuwar nasara a fannin samar da ci gaba mai inganci, dangane da falsafa da kimiyyar zamantakewa, ta yadda hakan zai samar da gudunmawar kaifafa basira, da karfin ingiza zamanantarwa irin ta Sin. (Saminu Alhassan)














Discussion about this post