Shugaban Hukumar Kula Da Shige Da Fice ta ƙasa (NIS), Isah Jere Idris ya bayyana cewa hukumar za ta ci gaba da duk wani ƙoƙari da ya wajaba wajen ganin ta magance cuwa-cuwa a ɗaukacin manya da ƙananan ofisoshinta.
Ya bayyana haka ne a yayin ƙaddamar da sabbin jami’an da aka naɗa a ɓangaren yaƙi da cin hanci da rashawa na hukumar ta NIS da ake wa laƙabi da (ACTU) a Abuja .
Ya ƙara da cewa, “Ba ni da buƙatar nanata batun yadda cin hanci ke ci gaba da zama ɗaya daga cikin annobar da ke kawo cikas ga bunƙasa da ɗorewar ƙasarmu. Abin ya zama ruwan dare a kusan dukkan sassan ƙasar. A wasu lokutan ma, abubuwa na cin hanci da rashawa sun zama tamkar wata yardajjiyar ɗabi’a a cikin al’umma.
“Wannan ba ƙaramin haɗari ne ba kuma ya kamata kowane mutum nagari ya yaƙi abin . Wajibi ne na faɗa muku cewa a matsayinku na ma’aikatan Sashen Yaƙi Da Cin Hanci na ACTU, kuna da jan aiki a gabanku saboda masu cin hanci za su riƙa ramuwar gayya a koyaushe amma kuma ina tabbatar muku da samun goyon bayan mahukunta domin ku samu sukunin gudanar da ayyukanku cikin nasara,” ya bayyana.
Sanarwar da ta fito daga Jami’in hulɗa da jama’a na NIS, ACI Amos Okpu ta ƙara da cewa CGI Isah Jere ya kuma yaba wa ƙoƙarin shugabannin Hukumar Yaƙi Da Rashawa ta ICPC bisa kyakkyawar alaƙar da ke tsakanin hukumomin biyu tare da yin kiran ɗorewar lamarin. Musamman ya jinjina wa yadda hukumomin suke haɗin gwiwa wajen inganta ƙwazon ma’aikata, kana ya bayyana cewa horas da ma’aikata da sake horas da su na da matuƙar muhimmanci wajen kawo ci gaban ma’aikata.
Tun da farko, Shugaban ICPC Farfesa Bolaji Owasoneye wanda Mista Abbia Udofia ya wakilta, ya yaba wa NIS bisa namijin ƙoƙarinta wurin kafa sashen yaƙi da cin hanci da daƙile gudanar da ayyuka marasa inganci. Ya yi kira ga waɗanda aka naɗa a sashen su fahimci aikin da aka ɗora musu alhakin gudanarwa inda ya nemi su zama ababen koyi da mayar da hankali kacokan a kan ayyukansu .
Daga cikin muhimman abubuwan da aka aiwatar a wurin har da rantsuwar kama aiki wanda Barista Abodurin Adebimpe, mataimakin Babban Sufiritanda na ICPC ya karanta musu suka amsa.
Bisa ƙaddamar da jami’an sashen na ACTU dai, doka ta ba su dama su sanya ido, da bincike tare da ba da rahoton duk wani abu na cin hanci a sassan hukumar ta NIS domin ɗaukar mataki.
Taron ƙaddamarwar ya samu halartar manyan mahukuntan NIS da manyan jami’an ICPC da suka haɗa da Mrs. Edu Davis, Babbar Jami’a a hukumar, da Larry Abwo da kuma Prisca Okwaraebo waɗanda dukkansu masu muƙamin Manyan Sufiritanda ne a ICPC da sauransu.
Ita dai Hukumar Kula Da Shige Da Fice ta Qasa (NIS) ta kasance a kan gaba wajen yaƙi da cin hanci da rashawa a tsakanin rundunonin Nijeriya masu sa kayan sarki bisa wasu muhimman abubuwa na yaki da rashawa da ta aiwatar kamar mayar da tsarin biyan kuɗin fasfo ta intanet, da cike takardun fom na neman fasfon da rajistar baƙin da ke shigowa cikin ƙasa da sauran takardu da hukumar ke bayarwa.