ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, September 11, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Shugabannin Sin Da Rasha Sun Yi Musayar Gaisuwar Sabuwar Shekara

by Sulaiman
8 months ago

A yau Laraba 31 ga Disamba, 2025, shugaban kasar Sin Xi Jinping da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin sun yi musayar gaisuwar sabuwar shekara.

Shugaban kasar Sin, a madadin gwamnati da al’ummar kasarsa, ya bayyana kyakkyawan fata ga shugaban kasar Rasha da al’ummar kasar. Xi Jinping ya nuna cewa, shekarar 2025 ita ce shekarar cika shekaru 80 da kafa MDD. Sin da Rasha sun shirya bikin cika shekaru 80 da samun nasarar yakin da Sinawa suka yi da mamayar dakarun Japan, da yakin kare tarayyar Soviet da kuma nasarar yakin duniya na adawa da tafarkin murdiyya, wanda ya bayyana niyyar duniya ta samun zaman lafiya da adalci.

Xi Jinping ya kuma nuna cewa, shekarar 2026 ita ce shekarar cika shekaru 30 da kafa dangantakar abokan hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare a dukkannin fannoni tsakanin Sin da Rasha da kuma shekarar cika shekaru 25 da rattaba hannu kan yarjejeniyar abota da hadin gwiwa tsakanin Sin da Rasha. Yana mai fatan ci gaba da tuntubar shugaba Putin, don hadin gwiwar shugabannin biyu wajen jagorantar dangantakar Sin da Rasha a sabon zamani da za ta ci gaba da samar da sabbin sakamako.

ADVERTISEMENT

A nasa bangare, shugaban kasar Rasha Putin ya mika cikakkiyar taya murnar sabuwar shekara ga Xi Jinping. Ya yi fatan samun farin ciki da koshin lafiya ga al’ummar Sinawa. Putin ya bayyana cewa, dangantakar abokan hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni a sabon zamani tsakanin Rasha da Sin ta ci gaba da samun sakamako masu yawa a shekarar da muke bankwana da ita. A shekara mai zuwa, kasashen biyu za su bude “shekarar ba da ilimi tsakanin Rasha da Sin” tare. Yana kuma fatan kara tuntubar Xi Jinping game da dangantakar kasashen biyu da manyan batutuwan kasa da kasa.

Duk dai a wannan rana, firaministan kasar Sin Li Qiang da takwaransa na kasar Rasha Mikhail Mishustin sun yi musayar gaisuwar sabuwar shekara. (Amina Xu)

LABARAI MASU NASABA

Sin Ce Ta Zo Ta Farko A Rahoton Yanayin Tsaron Jama’a Na Duniya

Sin Ta Ciri Tuta Game Da Rawar Gani Da Take Takawa A Fannin Warware Kalubalen Tsaro A Gabas Ta Tsakiya

Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Gwarzon Shekarar 2026 Abdulsamad Rabiu
  • Sulaiman
    Buƙatar Ɗaukar Matakan Daƙile Yaɗuwar Cutar Mashaƙo A Nijeriya
  • Sulaiman
    Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje
  • Sulaiman
    Sin Ce Ta Zo Ta Farko A Rahoton Yanayin Tsaron Jama’a Na Duniya

MASU ALAKA

Sin Ce Ta Zo Ta Farko A Rahoton Yanayin Tsaron Jama’a Na Duniya
Daga Birnin Sin

Sin Ce Ta Zo Ta Farko A Rahoton Yanayin Tsaron Jama’a Na Duniya

September 10, 2026
Sin Ta Ciri Tuta Game Da Rawar Gani Da Take Takawa A Fannin Warware Kalubalen Tsaro A Gabas Ta Tsakiya
Daga Birnin Sin

Sin Ta Ciri Tuta Game Da Rawar Gani Da Take Takawa A Fannin Warware Kalubalen Tsaro A Gabas Ta Tsakiya

September 10, 2026
Sin Da Amurka Na Gudanar Da Tattaunawa Dangane Da Yiwuwar Rage Harajin Ramuwar Gayya Wanda Darajarsa Ka Iya Kaiwa Dala Biliyan 30
Daga Birnin Sin

Sin Da Amurka Na Gudanar Da Tattaunawa Dangane Da Yiwuwar Rage Harajin Ramuwar Gayya Wanda Darajarsa Ka Iya Kaiwa Dala Biliyan 30

September 10, 2026
Next Post
Jam’iyyar NNPP Ta Yi Watsi Da Dakatarwar Da Aka Yi Wa Dungurawa A Kano

Jam'iyyar NNPP Ta Yi Watsi Da Dakatarwar Da Aka Yi Wa Dungurawa A Kano

LABARAI MASU NASABA

Dalilin Da Ya Sa Ba Zan Janye Wa Atiku Ba A Zaɓen 2027 – Peter Obi

September 11, 2026
Farashin Siminti Zai Ragu Idan Farashin Kayan Aiki Ya Sauka – BUA

Gwarzon Shekarar 2026 Abdulsamad Rabiu

September 11, 2026
Cutar Kwalara Na Ci Gaba Da Yi Wa ‘Yan Nijeriya Kisan Mummuƙe

Buƙatar Ɗaukar Matakan Daƙile Yaɗuwar Cutar Mashaƙo A Nijeriya

September 11, 2026
Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje

Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje

September 10, 2026
Sin Ce Ta Zo Ta Farko A Rahoton Yanayin Tsaron Jama’a Na Duniya

Sin Ce Ta Zo Ta Farko A Rahoton Yanayin Tsaron Jama’a Na Duniya

September 10, 2026
Sin Ta Ciri Tuta Game Da Rawar Gani Da Take Takawa A Fannin Warware Kalubalen Tsaro A Gabas Ta Tsakiya

Sin Ta Ciri Tuta Game Da Rawar Gani Da Take Takawa A Fannin Warware Kalubalen Tsaro A Gabas Ta Tsakiya

September 10, 2026
Gwamnatin Tarayya Ta Gwangwaje Tawagar Kwallon Kwando Ta Mata Da Dala 100,000 Kowace

Gwamnatin Tarayya Ta Gwangwaje Tawagar Kwallon Kwando Ta Mata Da Dala 100,000 Kowace

September 10, 2026
Sin Da Amurka Na Gudanar Da Tattaunawa Dangane Da Yiwuwar Rage Harajin Ramuwar Gayya Wanda Darajarsa Ka Iya Kaiwa Dala Biliyan 30

Sin Da Amurka Na Gudanar Da Tattaunawa Dangane Da Yiwuwar Rage Harajin Ramuwar Gayya Wanda Darajarsa Ka Iya Kaiwa Dala Biliyan 30

September 10, 2026
Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar da Shirin Ƙara Kuɗin Jarabawar WAEC da NECO

Gwamnatin Tarayya Za Ta Rika Bai Wa Ɗalibai 100MB Na Data Kyauta Kullum

September 10, 2026
Sin Da Amurka Na Wanzar Da Mu’amala Game Da Shirin Ganawar Da Manyan Shugabannin Kasashen Biyu Za Su Yi A Bana

Sin Da Amurka Na Wanzar Da Mu’amala Game Da Shirin Ganawar Da Manyan Shugabannin Kasashen Biyu Za Su Yi A Bana

September 10, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.