Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Mao Ning ta bayyana cewa, ya kamata bangaren Amurka ya bi ka’idar “kasar Sin daya tak a duniya” da kuma bukatun yarjejeniyoyi uku na Sin da Amurka, kuma ta yi taka tsan-tsan kan batun Taiwan, sannan ya daina aika mummunan sako ga ’yan awaren yankin Taiwan.
Mao Ning ta bayyana haka ne a gun taron manema labarai da aka gudanar yau da kullum, yau Talata.
Dangane da sanarwar da Indiya ta yi ta zayyana sunayen wurare 28, ciki har da yankunan kan iyakokin kasashen Sin da Indiya da ake takaddama a kansu, wadanda ke karkashin ikon mallakar Sin, Mao Ning ta bayyana cewa wannan matakin da bangaren Indiya ya dauka ba shi da tushen doka kuma ba shi da ma’ana.
Bugu da kari, da aka ambaci hare-haren yanar gizo, Mao Ning ta ce Sin ta dade da adawa da kuma yaki da ayyukan masu satar bayanai, a sa’i daya kuma tana adawa da bata wa Sin suna bisa batun tsaron yanar gizo.(Safiyah Ma)














