Kasar Sin ce ta mamaye teburin lambar yabo ta zinare a gasar nuna kwarewar aiki ta duniya karo na 48 da aka kammala jiya Lahadi da dare a birnin Shanghai, wannan ita ce gasa ta 5 a jere da kasar Sin ke lashe mafi yawan lambobin yabo.
Chen Jining, mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS, kuma sakataren kwamitin jam’iyyar na birnin Shanghai, da ‘dan majalisar gudanarwar kasar Sin Shen Yiqin, sun halarci bikin rufe gasar.
‘Yar kasar Sin He Xiaoman, ta samu lambar yabo mafi daraja ta alfarma ta Albert Vidal, saboda hazakar da ta nuna a gasar fasahar shimfida layin dogo. Wannan lambar karramawa ita ce mafi daraja da ake bayarwa ga ‘dan gasa mafi yawan maki a dukkan fannonin kwarewa.
Kasar Sin ta fafata a fannonin kwarewa 64, inda ta lashe lambobin zinare 41 da azurfa 11, sai tagulla 4 da kuma lambobin yabo na kwarewa guda 6. Tawagar kasar Sin ce ta zo ta daya da yawan lambobin zinare, kuma ita ce ta samu lambobin yabo mafi yawa, da ma yawan makin rukunoni, don haka ta zama mafi hazaka a gasar ta nuna kwarewar aiki ta duniya.
Kungiyar shirya gasar nuna kwarewa ta kasa da kasa ce ta shirya gasar da hadin gwiwar ma’aikatar kula da al’umma ta kasar Sin da gwamnatin birnin Shanghai. An gudanar da babban taro kan kwarewar aiki watau WorldSkills Conference na 2026 da kuma baje koli, yayin da ake gudanar da gasar. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)














