A yau Alhamis, ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin ta bayyana adawa mai karfi game da amfani da dandalolin mabambantan sassa kamar kungiyar G20 wajen kambama abin da aka kira da “rashin daidaiton tattalin arziki” da kuma “wuce gona da iri.”
Mai magana da yawun ma’aikatar, Huang Ling, ta bayyana hakan yayin da take amsa wata tambaya game da kalaman da sakataren baitulmalin Amurka, Scott Bessent, ya yi kwanan nan dangane da kasar Sin.
Huang ta ce, irin wadannan kalamai a zahiri wata hanya ce ta boye manufar gitta shingen kasuwanci tare da ba da uzurin matsin lamba da tarnake ci gaban kasar Sin.
Huang ta kuma bayyana cewa, Sin tana matukar adawa da takunkuman da Amurka take ta kakaba wa kamfanonin kasarta da kuma Sinawa saboda zargin alaka da Iran. Sin ta sha nanata adawarta da takunkumai na gaban-kai da ba su da tushe a dokokin kasa da kasa, kuma ba su samu amincewa daga kwamitin sulhu na MDD ba.
Kazalika, ta ce irin wadannan takunkumai suna yin katsalandan ga harkokin kasuwanci na yau da kullum, kana suna illata samun wadatar makamashi na duniya da kuma samar da makamashin ba tare da tangarda ba. (Abdulrazaq Yahuza Jere)














