Yau Alhamis rana ce ta cika shekaru 81 da samun nasara a yakin da al’ummar Sin suka yi da mamayar dakarun kasar Japan da kuma yakin duniya na kin tafarkin murdiya. A kwanan nan, ma’aikatar tsaro ta Japan ta fitar da takardar bayani ta tsaron kasa ta shekarar 2026, inda ta yi ikirarin cewa za ta kara neman “karfin kai hari kan sansanonin abokan gaba”.
Har ila yau, ma’aikatar tsaron kasa ta Japan ta gabatar da bukatar kasafin kudi na shekarar 2027, inda jimillar kudaden da ta nema ya kai kudin kasar Yen tiriliyan 8.89, wanda ya zama mafi girma a tarihi.
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Guo Jiakun, a taron manema labarai da aka saba yi da ya gudana yau, yayin da yake amsa tambaya game da ko matakan da Japan ke dauka suna kalubalantar sakamakon nasarar yakin duniya na biyu, ya bayyana cewa, tun da dadewa, masu ra’ayin rikau na Japan suna yunkurin sake rubuta tarihin mamaya, da kuma kubuta daga tsare-tsaren da kasa da kasa suka yi mata bayan yakin.
Guo ya jaddada cewa, kasarsa na yi wa masu ra’ayin rikau na Japan gargadin cewa, daukar nauyin alhakin kasa da kasa dake bisa wuyanta, da kawar da ra’ayin nuna karfin soji gaba daya, da kuma tsayawa kan samun ci gaba ta hanyar zaman lafiya, ita ce hanya madaidaiciya ga Japan.
A cewarsa, kasar Sin za ta hada kai da kasashen duniya masu son zaman lafiya, wajen dakile yadda “sabon salon ra’ayin nuna karfin soji” na Japan ke ci gaba da bunkasa karkashin sunan wai “mayar da kasa yadda take”, da tada zaune tsaye a yankin, har ma da cutar da duniya baki daya. (Bilkisu Xin)














