A jiya Laraba 23 ga watan Satumba, wakilin din-din-din na kasar Sin a MDD, Fu Cong ya yi kira ga al’ummar duniya da su karfafa hadin kai da hadin gwiwa a tsakaninsu, tare da bayar da muhimmanci ga tsarin tsaro da bunkasar fasahar AI domin moriyar dan’adam.
Fu Cong ya yi wannan kira ne lokacin da yake gabatar da jawabi a budadden taron majalisar tsaro kan kirkirarriyar fasahar AI da tsaron kasa da kasa.
Ya ce, ya kamata a ba da muhimmanci sosai kan yadda za a karkatar da fasahar AI zuwa yadda za ta bunkasa ci gaban dan’adam da tsaro, da kuma bayar da gudunmawa ga zaman lafiyar duniya da kwanciyar hankali da cigaba mai inganci. (Mai Fassara: Suleiman Suleiman)














