Ƙungiyar Kiristocin Arewa (NCA) ta goyi bayan Sarkin Musulmi, Muhammadu Sa’ad Abubakar III, kan kiran da ya yi ga ’yan siyasa da su daina amfani da kuɗin gwamnati ko kuɗin sata wajen zuwa aikin hajji.
Shugaban NCA, Rev. John Joseph Hayab, ya ce amfani da kuɗin da aka samu ta hanyar cin hanci da rashawa wajen zuwa aikin hajji zai ci karo da manufar ibadar.
Ya kuma goyi bayan kiran Sarkin Musulmi ya yi wa ’yan Nijeriya da su yi amfani da ƙuri’unsu wajen saukw ’yan siyasar da suka gaza samar da shugabanci na gari.
Hayab ya ce ’yan siyasa za su fi mayar da hankali kan ayyukansu idan sun san cewa masu zaɓe za su iya sauke su daga kan mulki idan ba su yi abin da ya kamata ba.
Ya kuma yi kira ga Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) da ta tabbatar da cewa an mutunta zaɓin masu kaɗa ƙuri’a.
Shugaban NCA ya ƙara da cewa ya kamata gwamnatoci su fi mayar da hankali kan gina hanyoyi, makarantu, inganta kiwon lafiya, samar da wutar lantarki da tsaro, maimakon kashe maƙudan kuɗaɗen gwamnati wajen tallafa wa aikin hajji.
Ya kuma yi gargaɗi kan yin addu’o’i a matsayin wata siga madadin yin aiki tuƙuru.
Ya bayyana cewa kamata ya yi a yi addu’a tare da aiki da kuma ɗaukar nauyin da ya rataya a wuyan shugabanni da ’yan ƙasa.














