Alkaluma daga ma’aikatar raya masana’antu da fasahohin sadarwa ta kasar Sin, sun nuna yadda kasar ta cimma nasarar kera daukacin sassan mutum-mutumin inji sama da samfura 400, adadin da ya haura rabin jimillar na duniya baki daya, ya kuma shaida saurin fadadar matsayin kasar a fannin kirar mutum-mutumin inji.
Alkaluman da ma’aikatar ta fitar a Litinin din nan, sun nuna cewa a rabin farko na shekarar nan ta 2026, adadin mutum-mutumin inji masu siffar kare da aka kera a kasar Sin, sun kai kaso 70 bisa dari cikin jimillar na duniya baki daya.
Kazalika, karuwar bukatun duniya game da kayayyakin kirkirarriyar basira ko AI, ya bunkasa yawan sassan na’urorin harhada latironi na IC da Sin din ke fitarwa zuwa sassan ketare, inda darajar ICn da kasar ke fitarwa a farashin kudin kasar wato yuan, ya karu da kaso 88.7 bisa dari kan mizanin shekara-shekara cikin watanni shida na farkon bana. (Mai fassara: Saminu Alhassan)














