Ranar 15 ga watan Agusta rana ce ta kare muhalli ta kasar Sin karo na 4. Albarkacin wannan rana Sin za ta gabatar da kundin dokar kare muhalli, wanda ya kasance irinsa na 2 a kasar Sin bayan kundin dokar dake shafar zaman rayuwar fararen hula da aka yi wa lakabi da “kundin doka”. Aiwatar da wannan doka zai alamanta cewa, aikin tsara dokokin muhalli na kasar Sin ya shiga sabon mataki, kuma ya kara karfafa tushen doka don zamanantar da al’umma bisa samun jituwa tsakanin dan Adam da muhallin halittu.
A ranar 12 ga watan Maris na bana, taro na 4 na majalisar wakilan jama’a ta Sin ta 14 ya zartas da kundin dokokin kare muhalli. Kundin ya kunshi sassa 5 da dokoki 1242, wanda ya hada da dokokin muhalli sama da 30 da tanade-tanaden gudanarwa fiye da 100, da tanade-tanaden dokokin mabambantan wurare cikin gida fiye da 1000. Sassan kundin dokokin suna kunshe da ka’idoji tanade-tanade, rigakafin gurbacewa da kare muhallin hallitu, da neman samun ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba, da rage fitar da hayaki mai dumama yanayi, da kuma tabbatar da doka kan masu laifi da kuma karin bayani.(Amina Xu)













