ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, October 25, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sojoji Sun Ceto Mutane 14 Da Aka Sace, Sun Ƙwato Bindigogi 2 A Kaduna Da Katsina

by Sadiq
4 weeks ago

Sojojin Operation FANSAN YAMMA sun daƙile wani hari na ’yan ta’adda, sun ceto mutane 14 da aka yi garkuwa da su, tare da ƙwato bindiga ƙirar AK-47 guda biyu a wasu samame da suka gudanar a jihohin Kaduna da Katsina.

Jami’in hulɗa da manema labarai na Operation FANSAN YAMMA, Lt. Col. Aliyu Danja, ya ce an gudanar da ayyukan tsakanin 23 da 25 ga watan Satumba 2026.

A Kaduna, sojoji sun yi wa ’yan ta’adda kwanton ɓauna a Rijana, ƙaramar hukumar Kachia, bayan samun bayanan sirri kan motsinsu.

ADVERTISEMENT

’Yan ta’addan sun tsere, inda sojojin suka ƙwato bindiga ƙirar AK-47, harsasai da wasu kayayyaki.

Sojojin sun kuma kama wani da ake zargi da hannu a ayyukan ’yan ta’adda a ƙauyen Awom, Kachia.

LABARAI MASU NASABA

EFCC Ta Buɗe Shafin Ɗaukar Ma’aikata Na 2026, Duba Sharuɗɗan Neman Aikin

Wa’adin INEC Ya Ƙare: Ina Makomar Takarar Aminu Gwarzo A Kano Da Pantami A Gombe?

An ce an same shi da bindiga ƙirar gida da harsasai bakwai.

A Katsina kuwa, sojoji sun kama wasu mutane uku da ake zargi da kai wa ’yan ta’adda kayan aiki a ƙaramar hukumar Faskari.

Rundunar ta ce mutanen suna ɗauke da Naira miliyan 2.7 da ake zargin kuɗin fansa ne, da wayoyi guda uku.

A ranar 25 ga watan Satumba, sojoji sun sake yi wa ’yan ta’adda kwanton ɓauna a Faskari.

Bayan sun tsere, sojojin sun ƙwato wata bindiga ƙirar AK-47, harsasai 30 da babur.

A wani samame na daban da suka kai Faskari, sojojin sun ceto mutane 14 da aka yi garkuwa da su, maza 12 da mata biyu.

An ce an sace mutanen ne daga ƙauyukan Anguwan Miko da Tafoki, amma ’yan ta’addan sun gudu sun bar su bayan sun ga sojojin na zuwa.

An miƙa mutanen da aka ceto ga hukumomin ƙaramar hukumar Faskari domin ɗaukar matakan da suka dace.

Rundunar ta kuma buƙaci jama’a su ci gaba da bai wa jami’an tsaro bayanan sirri kan duk wani motsi ko aiki da ake zargi.

MASU ALAKA

EFCC Ta Buɗe Shafin Ɗaukar Ma’aikata Na 2026, Duba Sharuɗɗan Neman Aikin
Manyan Labarai

EFCC Ta Buɗe Shafin Ɗaukar Ma’aikata Na 2026, Duba Sharuɗɗan Neman Aikin

October 25, 2026
Wa’adin INEC Ya Ƙare: Ina Makomar Takarar Aminu Gwarzo A Kano Da Pantami A Gombe?
Siyasa

Wa’adin INEC Ya Ƙare: Ina Makomar Takarar Aminu Gwarzo A Kano Da Pantami A Gombe?

October 25, 2026
Kwamitin Zartarwa Na ADC Na Ƙasa Ya Yi Watsi Da Bangaran David Mark Da Bala Gombe, Ya Naɗa Shugabancin Riƙo
Siyasa

ADC Ta Yi Wa APC Ba’a Kan Zargin Hayar Taron Jama’a Da Rashin Cika Kujeru A Taron Kaduna

October 25, 2026
Next Post
Ghana

Ghana Ta Fara Neman Hanyar Biyan Kudin Cinikayya Kai-tsaye Tsakaninta Da Sin

LABARAI MASU NASABA

EFCC Ta Buɗe Shafin Ɗaukar Ma’aikata Na 2026, Duba Sharuɗɗan Neman Aikin

EFCC Ta Buɗe Shafin Ɗaukar Ma’aikata Na 2026, Duba Sharuɗɗan Neman Aikin

October 25, 2026
SERAP Ta Kai Gwamnatin Nijeriya Kotu Kan Zargin Badakalar Naira Biliyan 78.8

SERAP Ta Kai Gwamnatin Nijeriya Kotu Kan Zargin Badakalar Naira Biliyan 78.8

October 25, 2026
Malaman Makarantun Gwamnati A Abuja Za Su Tsunduma Yajin Aiki Daga Ranar Litinin

Peter Obi, Marowaci Ne Ba Zai Iya Shugabancin Nijeriya Ba – Wike

October 25, 2026
Wa’adin INEC Ya Ƙare: Ina Makomar Takarar Aminu Gwarzo A Kano Da Pantami A Gombe?

Wa’adin INEC Ya Ƙare: Ina Makomar Takarar Aminu Gwarzo A Kano Da Pantami A Gombe?

October 25, 2026
Sojoji Sun Kuɓutar Da Mutane Uku Da Aka Sace A Kebbi

Sojoji Sun Kuɓutar Da Mutane Uku Da Aka Sace A Kebbi

October 25, 2026
Ana Buƙatar Ɗaukar Matakai Masu Tsauri Domin Ci Gaban Nijeriya – Wike

Ana Buƙatar Ɗaukar Matakai Masu Tsauri Domin Ci Gaban Nijeriya – Wike

October 25, 2026
Rundunar Sojin Nijeriya Ta Tura Dakarunta Yaƙi Da ‘Yan Bindiga A Yankin Olle-Bunu Na Jihar Kogi

Sojoji Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 15 Ta Harin Sama A Borno

October 25, 2026
2027: Hana Tinubu Wa’adi Na Biyu Na Iya Jefa Nijeriya Cikin Rikicin Siyasa — Pakistan

Tinubu Ya Cancanci A Sake Zaɓensa A 2027 — Pakistan

October 25, 2026
Amnesty Ta Yi Allah Wadai Da Harin Jihar Taraba Da Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutum 40

Amnesty Ta Yi Allah Wadai Da Harin Jihar Taraba Da Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutum 40

October 25, 2026
Kwamitin Zartarwa Na ADC Na Ƙasa Ya Yi Watsi Da Bangaran David Mark Da Bala Gombe, Ya Naɗa Shugabancin Riƙo

ADC Ta Yi Wa APC Ba’a Kan Zargin Hayar Taron Jama’a Da Rashin Cika Kujeru A Taron Kaduna

October 25, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.