Dakarun haɗin gwiwar sojojin Arewa maso Yamma, ƙarƙashin Operation Fansan Yamma, sun kama wani da ake zargi da aikata ta’addanci mai suna Auta Maikyala a garin Kagarko, Ƙaramar Hukumar Kagarko ta Jihar Kaduna. A lokaci guda, sojojin sun ƙara kai hare-haren ƙasa da na sama kan maboyar ƴan bindiga a Jihar Zamfara, ciki har da wuraren da ake zargin suna da alaƙa da fitaccen shugaban ƴan bindiga, Dogo Gide.
Kakakin yaɗa labarai na riƙon ƙwarya na rundunar, Kyaftin Tamuno Sinivie, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Juma’a, 6 ga Nuwamba, 2026. Ya ce an kama Auta Maikyala ne a ranar 5 ga Nuwamba, yayin da yake karɓar magani a wani asibiti da ke Kagarko, bayan ya samu raunin harbin bindiga a wani artabu da wata ƙungiyar ƴan bindiga da ke hamayya da su. Rundunar ta ce jami’an DSS sun taimaka wajen gudanar da samamen.
Binciken farko da rundunar ta ce ta gudanar ya nuna cewa ana zargin wanda aka kama da hannu a hare-hare kan al’ummomi, satar mutane da kuma satar shanu. A halin yanzu yana tsare a hannun jami’an tsaro domin ci gaba da bincike da kuma gurfanar da shi a gaban kotu. Sai dai rundunar ba ta bayyana cikakkun bayanai kan hare-haren da ake zargin ya aikata ba.
A wani samame na daban, sojojin sun gudanar da aikin share maboyar ƴan bindiga a ƙauyukan Aljummu Hausa, Aljummu Fulani da Tunga Magaji da ke Ƙaramar Hukumar Maradun ta Jihar Zamfara. Rundunar ta ce aikin ya kai ga rusa wasu maboyar ƴan bindiga, tare da takaita ayyukansu da inganta tsaro a yankunan da abin ya shafa.
Haka kuma, rundunar sojin saman Nijeriya ta kai hare-haren sama kan wasu wurare a Babban Doka da Dajin Kuyumbana da ke Ƙaramar Hukumar Maru, waɗanda ake zargin suna da alaƙa da Dogo Gide. Kyaftin Sinivie ya ce an kai hare-haren ne bayan samun bayanan sirri da ke nuna cewa ƴan bindiga na taruwa a yankin domin tsara hare-hare. Rundunar ta ce sojoji na ci gaba da mamaye yankin, tare da kira ga jama’a da su riƙa kai sahihan bayanai ga hukumomin tsaro.













