“China Haul”wato gabatar da bidiyon yayata abubuwan da aka saya daga kasar Sin ya shahara matuka a halin yanzu a shafukan sada zumunta a duniya. Baki daga kasashen waje suna zuwa da akwatuna marasa kaya, su cika da kayayyakin Sin, sannan su koma gida su yi bidiyon “China Haul’, inda jimillar kallon irin wadannan bidiyoyi a dandalin sada zumunta ya wuce miliyan 110.
A lokacin da, kayayyakin da ake fi sani na Sin su ne shayi da siliki, yanzu kuma, su ne jiragen sama marasa matuki, wayoyin da ake ninkewa da kayayyakin kwalliya na Sin da kayan wasa na zamani da sauransu. To, wadanne abubuwa ne kuma za su jawo hanklin baki nan gaba don gabatar da bidiyon “China Haul”?Da misalin bikin Canton Fair karo na 140 da aka kammala kwanan nan, watakila za a iya amsa wannan tambaya.
A wannan bikin, rumfunan mutum-mutumin injin ba da hidima masu sarrafa kansu da na’urorin gida masu sarrafa kansu da jiragen sama marasa matuki, sun sami karbuwa sosai. Masu sayayya sun yi layi a gaban rumfunan don gwada kayayyakin, yayin da masu sama da kaya suka yi ta tuntubar abokan ciniki. Abin da aka nuna a wannan biki, kayayyakin kirkire-kirkiren fasaha ne da kamfanonin Sin ke iya samarwa a halin yanzu, amma ba su da yawa a kasuwa tukuna.
Wannan shi ne karo na uku da Max Young, wani mai sayayya dan Biritaniya, ya zo bikin Canton Fair. A wannan karo ya taho da mahaifiyarsa Susanna Elliot, wadda ke dogaro da keken guragu a yau da kullum saboda ciwon shan inna. Ma’aikata sun taimaka mata sanya na’urar dake taimaka wa mutum tafiya, sannan ta tashi a hankali, ta yi tafiya, har ma ta dan hau matakala.
Nan take Max ya sayi wannan na’urar, kuma ya ce:“A Biritaniya da Turai, ban taba ganin irin wannan na’ura ba.”Wannan na’urar da Max ya saya, daya ce daga cikin kayayyaki da aka nuna a bikin Canton Fair. Masu sayayya da yawa sun kewaye mutum-mutumin injin ba da hidima masu sarrafa kansu, inda suka yi ta tambaya kan bayanan na’urori da tattauna batun yin oda. Wadannan kayayyaki suna da alama iri daya, wato fasaharsu na bunkasa yadda ya kamata kuma farashin ya ragu, ba ma kawai ana iya ganinsu a rumfar baje koli ba, za kuma a iya sayen su a kasuwa.
Jiragen sama marasa matuki da wayoyin da ake ninkewa da suka shahara a bidiyon “China Haul” a yanzu, su ma sun bi irin wannan hanya. Shekaru kadan da suka wuce, su ma sabbin kayayyaki ne da aka baje koli a bikin Canton Fair, yanzu kuma sun zama abin da ake yawan gani a bidiyon “China Haul” a kasashen waje. Na’urar da ke taimaka wa mutum tafiya da mutum-mutumin inji na ba da hidima masu sarrafa kansu da ake baje kolinsu a yau, a nan gaba za su iya zama “kayan al’ajabi da na saya a Sin” a cikin bidiyon.
Daga rumfa zuwa kasuwa, ta wannan hanya muke iya ganin karfin nazari da saurin samar da kayayyaki a nan kasar Sin. Dalilin da ya sa Sin ke iya samar da ingantattun kayayyaki da ake nunawa a cikin bidiyon “China Haul”, shi ne yawan kudaden da take zubawa cikin dogon lokaci ga nazarin kimiyya da fasaha. A shekarar 2025, yawan kudaden da Sin ta zuba a wannan fanni ya zarce yuan tiriliyan 3.9, kuma cikin shekaru biyar da suka gabata a jere, matsakaicin saurin karuwarsa ya wuce na Amurka, Japan da Jamus, wanda ya ingiza ingantacciyar bunkasuwar fasaha.
Daga fasaha zuwa kayayyaki kuma, Sin ta bayyana saurinta, kamfanonin lantarki a Shenzhen suna iya “tsara kayayyaki da safe, a yi gwajin samfurinsa da yamma, kuma a samar a kashe gari, tare da fitarwa ketare cikin mako guda”.Yayin da fasaha ke samun inganci cikin sauri, farashi yana raguwa da sauri, kuma kayayyaki suna shiga kasuwa da sauri. Abin da za a iya gani a bikin Canton Fair, shi ne abin da kamfanonin Sin ke iya samarwa.
Daga kayayyakin rumfunan bikin Canton Fair zuwa wadanda ake nuna su a bidiyon “China Haul”, abin da ke cikin akwatunan baki ba wai kayayyakin da suka shahara a yanzu ba ne kawai, akwai kayayyakin kirkire-kirkire da Sin ke samar da su a kai a kai bisa bukatun duniya, kuma kayayyakin fasaha kirar Sin suna amfana wa jama’ar duniya baki daya. (Marubuciya: MINA)













