ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, November 7, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Takarata Ba Ko A Mutu Ko Ai Rai Ba Ce – Gwamnan Kano

by Abubakar Sulaiman
47 seconds ago
Kano

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa burinsa na sake tsayawa takara domin neman wa’adi na biyu a zaɓen 2027 ba lamari ne da zai mayar da shi gwagwarmayar a mutu ko ai rai ba ne. Gwamnan ya ce mulki na hannun Allah, wanda yake bayar da shi ga wanda Ya so, kuma yake karɓewa a lokacin da Ya so.

Abba Yusuf ya bayyana hakan ne ranar Juma’a, 6 ga Nuwamba, 2026, yayin rantsar da sababbin kwamishinoni biyu, Sanusi Bature Dawakin Tofa, wanda aka naɗa a matsayin Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida, da Balarabe Sa’idu Gani, Kwamishinan Ma’adanai. Ya buƙaci masu kallon siyasa a matsayin fafatawar rayuwa da mutuwa su sake tunani, yana mai cewa dole ne ƴan siyasa su amince da ƙaddara.

Gwamnan ya waiwayi zaɓukan 2019 da 2023, inda ya ce duk da koma bayan da tawagarsa ta fuskanta a zaɓen 2019, sun amince cewa lokacin da Allah Ya ƙaddara musu na samun mulki bai yi ba. Ya kuma ce zaɓen gwamnan Kano na 2023 ya fuskanci ƙalubalen shari’a har zuwa Kotun Ƙoli, amma sun yi imanin cewa nasarar da suka samu ƙaddara ce daga Allah. Ya jaddada cewa makomar zaɓen 2027 tana hannun Allah.

ADVERTISEMENT

Bayan rantsar da kwamishinonin, gwamnan ya buƙaci Sanusi Bature ya inganta hanyoyin yaɗa manufofi da shirye-shiryen gwamnati, tare da ƙarfafa wayar da kan matasa kan illolin shan miyagun ƙwayoyi. Haka kuma, ya umurci Balarabe Sa’idu Gani da ya ƙarfafa sa ido da aiwatar da dokoki domin daƙile haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba, tare da haɗin gwiwa da hukumomin tsaro da jawo hankalin masu zuba jari.

Gwamnan ya kuma bayyana cewa gwamnatinsa ta kafa cibiyar sintiri da agajin gaggawa mai kayan aiki, wadda ke da sashin karɓar kira da umarni na sa’o’i 24, wadda ke da sashin tattara bayanan sirri da ɗakunan gwaje-gwaje na binciken ƙwayoyi. Ya ce cibiyar za ta bai wa mazauna jihar damar aika hotuna, bidiyo da saƙonnin murya cikin sirri domin taimakawa hukumomi wajen tattara bayanan tsaro.

LABARAI MASU NASABA

Za Ku Sha Jar Miya A Zangona Na Biyu – Tinubu

Ba Don Sauye-Sauyen Tattalin Arziƙin Da Muka Yi Ba, Da Darajar Naira Ta Ruguje – Tinubu

Kano
Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Za Ku Sha Jar Miya A Zangona Na Biyu – Tinubu
  • Abubakar Sulaiman
    Tinubu Ya Yi Wa Peter Obi Shaguɓe Kan Matsalar Zaizayar Ƙasa A Anambra
  • Abubakar Sulaiman
    Ba Don Sauye-Sauyen Tattalin Arziƙin Da Muka Yi Ba, Da Darajar Naira Ta Ruguje – Tinubu
  • Abubakar Sulaiman
    Barazana Ko Tsoratarwa Ba Zai Sa Na Janye Daga Takara Ba – Atiku

MASU ALAKA

Za Ku Sha Jar Miya A Zangona Na Biyu – Tinubu
Manyan Labarai

Za Ku Sha Jar Miya A Zangona Na Biyu – Tinubu

November 7, 2026

Sin Ta Kasance Abokiya Ga Kasashen Afirka Da Suka Fi Amincewa Da Dogaro Da Ita

Sin Ta Kasance Abokiya Ga Kasashen Afirka Da Suka Fi Amincewa Da Dogaro Da Ita

November 6, 2026
Daga Rumfar Baje Koli Zuwa“China Haul”—Bari Mu Leka Dalilin Da Ya Sa Sin Ke Iya Samar Da Ingantattun Kayayyaki Masu Araha A Duniya

Daga Rumfar Baje Koli Zuwa“China Haul”—Bari Mu Leka Dalilin Da Ya Sa Sin Ke Iya Samar Da Ingantattun Kayayyaki Masu Araha A Duniya

November 6, 2026
Xi Jinping Ya Gana Da Twakaransa Na Gabon

Xi Jinping Ya Gana Da Twakaransa Na Gabon

November 6, 2026
Juyin Mulki: Kotu Ta Yi Watsi Da Iƙirarin Azabtar Da Waɗanda Ake Zargi, Ta Amince Da Bayanan Da Suka Bayar

Shari’ar Zargin Juyin Mulki: Me Ya Shigar Da Bidiyon Binciken Sojoji Kotu?

November 6, 2026
Shawarwarin Sin Na Ci Gaba Da Ingiza Sabon Kuzari Wajen Rayawa Da Jagorantar Harkokin Intanet A Duniya

Shawarwarin Sin Na Ci Gaba Da Ingiza Sabon Kuzari Wajen Rayawa Da Jagorantar Harkokin Intanet A Duniya

November 6, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.