Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da takwaransa na Gabon Brice Nguema, wanda ke ziyarar aiki a kasar Sin, yau Juma’a a birnin Beijing. Shugabannin biyu sun kuma sanar da daga darajar dangantakarsu zuwa ta al’ummar Sin da Gabon mai makoma ta bai daya a sabon zamani.
Yayin ganawar, shugaba Xi ya bayyana cewa, Sin da Gabon na da tsare-tsaren da suka dace da juna, wadanda ke da muhimman damarmamakin hadin gwiwa.
Ya bukaci bangarorin biyu su fadada tare da daukaka hadin gwiwar cinikayya da zuba jari da ke tsakaninsu, domin bunkasa raya ayyukan masana’antu da samar da aikin yi da inganta rayuwar jama’ar Gabon, tare da karfafa wa kasar raya tattalin arzikinta da kanta.
A nasa bangare, shugaba Nguema ya yi matukar yaba wa yadda Sin ke yayata muhimmancin cudanyar bangarori daban-daban da kudurinta na tabbatar da adalci da daidaito a harkokin kasa da kasa da na shiyya.
Ya ce a shirye Gabon take ta hada hannu da Sin wajen karfafa goyon bayan juna da hadin gwiwa tsakanin Sin da Afrika, da aiki tare domin kare muradun kasashe masu tasowa. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)












