Sojojin Operation Hadin Kai (OPHK) na Rukunin Hadin Gwiwar Arewaci maso Gabas sun kama wani mutum da ake zargin babban mai sayar da miyagun kwayoyi ga ‘yan ta’adda na Boko Haram da ISWAP ne da ke aiki a wasu sassan Borno da Adamawa.
An gano wanda ake zargin da suna Zubairu Muhammad, mai shekaru 45, an kama shi da misalin karfe 6:30 na safe a ranar Talata da ta gabata, ta hannun sojojin 232 Battalion (Tactical), Uba, Jihar Adamawa.
- Akwai Bukatar Karfafa Hadaka Domin Ciyar Da Tashoshin Jiragen Ruwa Gaba A Afirka —Dantsoho
- Gwamnan Neja Ya Yi Allah-Wadai Da Sace Ɗaliban St. Mary A Papiri
Majiyoyi sun bayyana cewa Muhammad yana daga cikin manyan masu sayar da cannabis satiba da crystal meth (ICE) ga ‘yan ta’adda ta hanyar hanyoyin Askira-Uba, Chibok, Michika da Damboa.
A cewar wata majiya, sojojin sun kwato kulli 14 na cannabis satiba da aka kiyasta darajarsu sama da Naira miliyan 1, da kuma gram 43 na ICE, wanda aka kiyasta darajarsu fiye da Naira miliyan 3 daga hannun wanda ake zargin.
Haka kuma, an same shi da rigunan soja biyu na lebaka (camouflage T-shirts), wadanda ake zargin yana amfani da su yayin kawo miyagun kwayoyi ga ‘yan ta’adda.
Majiyar ta ce binciken farko ya kammala, kuma za a mika kayan da aka kwato ga Hukumar Kula da Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA), Rukuni na Yola don daukar mataki na gaba.














