ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Shin Tinubu Ya Tabbatar Da Sauke Ribadu Daga Mukaminsa?

by Shuaibu Shuaibu
2 weeks ago
Tinubu

Shugaban kasa, Bola Tinubu na son tsarin bai-daya wanda zai karfafa hada kai tsakanin sojojin Nijeriya, jami’an leken asiri da sauran hukumomin tsaro. A cewar mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga, wannan shi ne babban umarnin da shugaban kasa ya bayar a taron majalisar zartarwa ta tarayya (FEC) na ranar Laraba.

Shugaban kasa ya umarcin gaggawa na shirya cikakken tunkarar barazanar kasa da shirin ayyukan tsaro na shekaru biyar da ke gudana don tunkarar kalubalen tsaro masu tasowa a Nijeriya.

Amma umarnin bai tsaya ga kimantawa, manufofi, da dabaru kawai ba, watakila sakon ya fi tasiri da aika ga wanda ke jagorantar tawagar tsaron kasa ta gwamnatin tarayya.

ADVERTISEMENT

Tambaya ce da ba a samu amsa ba lokacin da Shugaba Tinubu ya nada Mejo Janar Adeyinka Famadewa a matsayin mashawarci na musamman kan harkokin tsaron kasa. A yawancin kasashe, tsaron kasa yana wakiltar abin da ake kira harkokin cikin gida da ofishin gida a Birtaniya. Amma da hade sojojin kasa da kuma kirkirar dabarun tsaro a wannan sabon mukami, abun da yake a zahiri aikin Adeyinka Famadewa da ikon ofishinsa ya bayyana.

A karkashin umarnin shugaban kasa na makon jiya, an mika aikin shirin tsaro ga Famadewa, don daidaita kwamiti mai matakin koli da ke da alhakkin tsara shirin da kuma samar da tallafin sakateriya.

LABARAI MASU NASABA

Buni Ya Nuna Kwarewarsa Ta Diflomasiyya

Kwairanga Ya Kafa Tarihi A Shugabancin Hukumar Kula Da Kasuwar Hannun Jari Ta Nijeriya

Dukkan jami’an tsaro da aikin leken asiri, daga Nuhu Ribadu zuwa ministan tsaro, shugabannin tsaro da daraktocin SSS da NIA za su rika bayar da rahoto kai tsaye ga Famadewa. Ba a fada wannan a fili ba. Amma ba za a iya musun cewa ana nufin haka ba.

Zai iya yiwuwa cewa fadar shugaban kasa ba ta jin dadin yadda ake samun ci gaba a cikin huldar diflomasiyya tsakanin Nijeriya da Amurka, ko wata kala ba jin dadi yadda Amurka ke kallonta.

Gaskiyar magana ita ce, bayan kowace mu’amala ko duk lokacin da mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaron kasa, Nuhu Ribadu ya ziyarci Washington, Shugaban kasa Tinubu na fitar da sabon umarni. Shin me ya sa lokacin ne kawai abin ke faruwa?

An yi zama har sau biyu na rukunin aikin hadin gwiwar Amurka da Nijeriya, wanda aka kafa bayan Shugaba Donald Trump na Amurka ya sanya Nijeriya a matsayin kasa ta musamman da ake damuwa da ita.

Ganawar farko na tawagar ya faru a Abuja a ranar 22 ga Janairu, 2026, inda sakatariyar harkokin siyasa ta Amurka, Allison Hooker, ta jagoranci wata tawaga ta ma’aikatun takwas.

Kuma a farkon watan Mayu 2026, Ribadu ya jagoranci tawagarsa zuwa Amurka don duba alkawuran tawagar hadin gwiwa, inda suka gana da mataimakin shugaban Amurka, JD Bance da sakataren harkokin waje, Marco Rubio, da Allison Hooker.

Bayan ‘yan kwanaki, Shugaba Bola Tinubu ya nada Famadewa a matsayin mashawarcinsa na musamman kan tsaron kasa. Zama na biyu na tawagar ya gudana a mako guda da suka gabata.

Kwana kadan daga baya, an ba Famadewa aikin shirya tsarin tsaron kasa tare da dukkan tsarin tsaro, kuma sakataren gwamnatin tarayya ya umurce shi da ya yi hadin gwiwa da mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaron kasa, don ka da a sami rudani.

Tinubu
Shuaibu Shuaibu
+ postsBio
  • Shuaibu Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/shuaibu-shuaibu/
    Buni Ya Nuna Kwarewarsa Ta Diflomasiyya
  • Shuaibu Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/shuaibu-shuaibu/
    Akwai Ayar Tabaya Kan Zuba Hannun Jarin Dala Miliyan 750 Na Yari
  • Shuaibu Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/shuaibu-shuaibu/
    Wa Tanimu Turaki Ke Fafutukar Karewa?
  • Shuaibu Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/shuaibu-shuaibu/
    Kwairanga Ya Kafa Tarihi A Shugabancin Hukumar Kula Da Kasuwar Hannun Jari Ta Nijeriya

MASU ALAKA

Zanga-Zanga: Gwamnatin Yobe Ta Bayar Da Umarnin Rufe Makarantun Jihar
Bakon Marubuci

Buni Ya Nuna Kwarewarsa Ta Diflomasiyya

August 28, 2026
Kwairanga Ya Kafa Tarihi A Shugabancin Hukumar Kula Da Kasuwar Hannun Jari Ta Nijeriya
Bakon Marubuci

Kwairanga Ya Kafa Tarihi A Shugabancin Hukumar Kula Da Kasuwar Hannun Jari Ta Nijeriya

July 24, 2026
Yadda Kotun Daukaka Kara Ta Kama Hanyar Cin Gashin Kanta
Bakon Marubuci

Yadda Kotun Daukaka Kara Ta Kama Hanyar Cin Gashin Kanta

July 24, 2026
Next Post
Tinubu

Gwamna Radda Ya Samu Lambar Yabo Kan Bunƙasa Tattalin Arziƙin Mata

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.