An haifi shugaban kasar ta Sudan Omar al-Hassan Ahmad Bashir a shekara ta 1945 a garin Hoshe Bannaga mai tazarar kilomita 100 daga yankin Arewa maso Gabashin birnin Khartoum.
Ya kuma fara karatunsa na babar makarantar Middile ta Ahlia dake garin Shendi, daga nan ne kuma mahaifansa suka yi kaura zuwa birnin Khartoum a can din kuma ya kammala iliminsa na sakandre.
Shugaban kasar dai ta Sudan ya ci gaba da daukar nauyin karatunsa ne da irin taimakon da yake samu na kudade daga mahaifansa da kuma dan abin da yake samu a lokacin da ya yi aiki a wani garejin gayaran motoci a birnin na Khartoum.
Bayan da shugaban kasar ta Sudan Omar al-Bashir ya kammala iliminsa na sakandre, ya shiga makarantar horar da sojin sama ta kasar Sudan, inda har ya sami horo na tuka jirgin sama.
A nan din ne kuma sami baban mukami a tskanin dakarun saman kasar Sudan, kafin kuma daga bisani ya zama shugaban Brigade din sojojin kasa na kasar Sudan.
Tsohon shugaban Kasar Sudan Omar Hassan Ahmad al-Bashir, ya sami manyan degrori biyu na Masters a fanin kimiyyar ayyukan soji, a kwalegen horars da kwamandojin soji ta Sudan da kuma kasar Malaysiya.
Haka zalika al-Bashir ya halarci kwalejin horas da soji ta birnin Cairo,inda har ya shiga cikin sojin kasar Masar, a lokacin da masar din ta yi yaki da Isra’ila a shekara ta 1973.
A shekara ta 1988, an nada Omar al-Bashir kan mukamin kwamandan Birgde ta 8 ta sojin Sudan a yankin Kudancin Sudan, inda aka dora masa alhakin yaki da yan tawayen Kudancin Sudan.
A watan Yuni na 1988 shida wasu manyan hafsoshin soji, sun hambarar da zababbiyar gwamnatin hadin kan kasa, karkashin shugabancin Sadik Al-Mahdi.
Manufofin gwamnatin Al-Bashir game da dabaka tsarin shariar musulunci a Sudan, ta haifar masa da rashin fahimtar juna tsakaninsa da alumomin Kudancin Sudan da mafi yawansu suka kasance Kiristoci, wanan dalili ne ma ya kara rura wutar fadan yan tawayen Kudancin Sudan.
A lokacin da Janar al-Bashir ya karbi ragamar mulkin Sudan ta hanyar juyin mulki irin na soji a ranar 30 ga watan Yunin 1989, an rika tabbatar da cewa anya al-Bashir zai iya rike ragamar mulkin kasar ta Sudan da yakin basasa ya daidaita.
A lokacin da al-Bashir ya karbi ragamar mulkin Sudan yana da shekaru 42 a duniya, kuma shi ne din ke zaman jami’in soji na farko da suka taka muhimiyar rawa wajen kai farmaki kan alumomin Kudancin Sudan.
Kasar dai ta Sudan an kasa ta kashi biyu, tsakanin Larabawa Musulmi na Arewaci da kuma kiristoci dake zaune a Kudancin na Sudan.
Kungiyar ‘yan tawayen Sudan ta SPLA ta fara yakin neman ‘yanci ne a shekara ta 1983, kuma tun daga wanan lokacin ne, kafin ma mulkin al-Bashir gwamnatocin da suka gabata, sun yi yaki da ‘yan tawayen Kudancin Sudan.
Kungiyar Afuwa ta Duniya ta kiyasta cewa, kimanin al’ummar kasar ta Sudan miliyan daya suka rasa rayukan su, sakamakon yakin basasar da ya barke a kasar, yayin kuma al’ummar ta Sudan miliyan 4.5 suka yi gudun hijira, zuwa wasu kasahe na ketare don tsira da rayukansu.
A lokacin da al-Bashir ya karbi ragamar mulki daga Sadek al-Mahdi a shekara ta 1989, da sunan ceto kasar Sudan daga hali na kaka na ka yi da ta sami kanta a ciki, ya sami goyon bayan Hassan al-Turabi shugaban jama’iyar National Islamic Front, kafin kuma daga karshe suka raba gari da juna, a lokacin da al-bashir ya rushe majalisar dokokin Sudan, ya kuma dauki matakai na soke dukanin jama’iyun siyasa dama kafofin yada labarun Sudan.