An gudanar da taro kan zamanantar da kasashe masu tasowa na 2026, a birnin Alkahiran Masar, inda aka yi masa taken “Tasowar Fasahar AI: Damarmaki da Kalubalen Zamanatar da Kasashe Masu Tasowa.”
Sama da masana da malamai 100 daga kasashe da yankuna 30 ne suka halarci taron da ya gudana jiya Laraba. A cewar mahalartan, kirkire-kirkire a fannin fasahar AI na gabatar da dimbin damarmaki, yayin da kuma yake tattare da kalubalen shugabanci.
A yayin taron BRICS na 18 da ya gudana a farkon watan Satumba, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gabatar da muhimman shawarwari domin amfani da AI wajen karfafa sabon tsarin ayyukan masana’antu da inganta samar da AI mai budadden tsari da ci gaban AI na bai daya, wadanda suka zayyana alkiblar raya fasahar AI da za ta yi kyakkyawan tasiri ga kowa.
Mahalarta taron sun kara da cewa, fasahar AI wata haja ce ta dukkan jama’a, suna masu bukatar kasashe masu tasowa su yi amfani da wannan gagarumar dama domin amfani da AI wajen karfafa mabambantan masana’antu da inganta rayuwar jama’a.
Sun kuma yi kira da a inganta shugabantar fasahar AI a duniya da aiwatar da hadin gwiwa na hakika tsakanin bangarori da dama da cike gibin da ke akwai a fannin AI da tabbatar da ci gaba da tsaro suna tafiya tare, kafada da kafada. (Fa’iza Mustapha)














