ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tawagogin Sin Da Amurka Sun Zurfafa Tattaunawa Game Da Batutuwan Raya Tattalin Arziki Da Cinikayya

by CGTN Hausa and Sulaiman
6 months ago
Amurka

Tawagogin kasar Sin da na Amurka sun gudanar da tattaunawa mai zurfi da ma’ana, sun kuma yi musayar ra’ayoyi da shawarwari dangane da batutuwan tattalin arziki da cinikayya da kasashen biyu suke mayar da hankali a kansu, ciki har da tsare-tsaren harajin fito, da ingiza dangantakar cinikayya da zuba jari, tare da wanzar da sakamako na matakai da suka amincewa bayan tattaunawa.

Jagororin tattaunawar ta wannan karo da ta gudana a ranakun Lahadi da jiya Litinin, sun hada da jagoran tawagar Sin, kuma mataimakin firaministan kasar He Lifeng. Sai kuma bangaren Amurka da ya hada da sakataren baitul-malin kasar Scott Bessent, da wakilin cinikayyar Amurka Jamieson Greer.

Da yake tsokaci yayin sabon zagayen tattaunawar, He Lifeng ya ce, karkashin kyakkyawan tsari na muhimmiyar fahimtar juna tsakanin shugabannin kasashen biyu, da sakamakon zagaye biyar na tattaunawar tattalin arziki da cinikayya da suka gudanar cikin shekarar da ta gabata, Sin da Amurka sun cimma jerin nasarori a fannonin raya tattalin arziki da na cinikayya.

ADVERTISEMENT

He ya ce, wadannan sakamako sun ingiza babban yanayi na tabbas, da daidaito cikin dangantakar tattalin arziki da cinikayya tsakanin sassan biyu, da ma tattalin arzikin duniya baki daya. Mataimakin firaministan na Sin ya kara da cewa, har kullum kasar Sin na adawa da matakin kakaba haraji daga bangare guda da Amurka ke aiwatarwa. Yana mai kira gare ta da ta kawar da dukkanin irin wadannan haraji, da ma sauran matakai masu haifar da tarnaki. A cewarsa, Sin za ta aiwatar da matakai na wajibi domin kare halastattun hakkoki da moriyarta.

Kazalika, Sin na fatan Amurka za ta rungumi tafarki na bai daya tare da Sin, ta kuma yi biyayya ga kudurorin musamman da shugabannin kasashen biyu suka cimma, tare da fadada fannonin hadin gwiwa, da takaita matsalolin da suke fuskanta, ta yadda hakan zai ingiza bunkasar alakar tattalin arziki, da cinikayya mai inganci da daidaito tsakanin kasashen biyu.

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Wakilai daga bangaren Amurka kuwa, sun ce daidaito a yanayin alakar tattalin arziki, da cinikayya tsakanin Sin da Amurka, na da matukar muhimmanci ga kasashen biyu da ma duniya baki daya, zai kuma tallafa matuka wajen bunkasa tattalin arzikin duniya, da samar da kariya ga tsarin rarraba hajoji zuwa sassan kasa da kasa, da daidaito ga hada-hadar kudade. Bangaren na Amurka, ya kuma bayyana bukatar magance takun-saka, da dakile kara ta’azzarar halin da ake ciki, da warware bambance-bambance ta hanyar gudanar da shawarwari.

Bugu da kari, sassan biyu sun amince da su nazarci kafuwar tsarin gudanar da hadin gwiwa, don ingiza alakar cinikayya da zuba jari, da ci gaba da amfani da tsarin na tattaunawa, da karfafa shawarwari, da tuntubar juna, da kyautata salon warware sabani, da fadada hadin gwiwa na zahiri, da ingiza alakar tattalin arziki da cinikayya mai dorewa, inganci da nagarta.

A ranakun Lahadi da jiya Litinin, bangarorin Sin da Amurka sun gudanar da tattaunawar kasuwanci a birnin Paris na Faransa. Yayin zantawar, wakilin musamman na kasar Sin kan harkokin cinikayya, kana mataimakin ministan kasuwancin kasar Li Chenggang ya bayyana cewa, a kwana daya da rabi, tawagogin bangarorin biyu sun gudanar da tattaunawa ta gaskiya kuma mai zurfi. Kana an cimma matsaya daya a matakin farko kan wasu batutuwa, kuma a mataki na gaba bangarorin biyu za su ci gaba da tafiyar da tsarin tattaunawar.

Li Chenggang ya ce, a wannan tattaunawa, bangarorin Sin da Amurka sun kara gane cewa, dangantakar ciniki cikin kwanciyar hankalin tsakanin kasashen biyu, tana amfanar da bangarorin biyu, har ma da duniya baki daya.

Amurka
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa
Amurka
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
  • Sulaiman
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

MASU ALAKA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
Daga Birnin Sin

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026

Next Post
Zargin Cin Hanci: Babu Wani Shirin Tsige El-Rufai – Kakakin Majalisar Dokokin Kaduna

El-Rufai Ya Zargi ICPC Da DSS Kan Tsare Shi Ba Bisa Ƙa’ida Ba Da Neman Ya Yi Ritaya Daga Siyasa

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.