Wani bincike kan ra’ayoyin jama’a da cibiyar bincike ta Pew ta kasar Amurka ta gudanar kwanan nan ya nuna cewa, idan aka kwatanta da sakamakon bincike da aka gudanar a shekarar 2024, yawan mutane masu goyon bayan kasar Amurka ya ragu a dukkan kasashen Najeriya, da Ghana, da Kenya, da Afirka ta Kudu, yayin da yawan mutanen da ke da ra’ayi mai kyau game da kasar Sin ke karuwa. Wannan sauyi ba kawai yake da alaka da bambancin manufofin hulda da kasashen waje na kasar Sin da na Amurka ba, har ma akwai nasaba da tattalin arziki, musamman ma fannin zuba jari.
Bisa wani rahoton da hukumar binciken yanayin tattalin arziki na kasar Amurka ko USBEA ta fitar a baya-bayan nan, zuwa karshen shekarar 2025, adadin kudin jari da kasar Amurka ta zuba wa nahiyar Afirka ya ragu zuwa dala biliyan 37.9, jimilla ce mafi kankanta tun daga shekarar 2008, wadda ta ragu da kaso 45.1% daga jimilla mafi yawa da aka samu a shekarar 2014. Yayin da alkaluma daga kasar Sin suka nuna cewa, tsakanin shekarar 2013 da ta 2024, jarin da kasar Sin ta zuba a kasashen Afirka kai tsaye ya yi ta samun karuwa, inda jimillar ta karu daga sama da dala biliyan 20 zuwa kimanin dala biliyan 43.8.
Bayan bambancin yawan jarin da Sin da Amurka suka zuba a nahiyar Afirka, bambancin kason jarin da suka kebe ma Afirka cikin dukkan kudin da suka zuba wa kasashen waje, shi ma abin lura ne. Bisa alkaluman da hukumar USBEA ta gabatar, cikin shekaru arba’in da suka gabata, kason kudin da Amurka ta zuba wa Afirka cikin dukkan jarin da kasar ta zuba a ketare, mafi yawa shi ne 2.57%, mafi kankanta kuma ya kasance 0.53%. Ta hakan za mu san cewa, ko da a lokacin da jimillar kudin da Amurka ta zuba ta kai matsayin koli, Afirka ba ta taba zama wata kasuwa mai muhimmanci a fannin zuba jari ga kasar Amurka ba. Sabanin haka, alkaluman da kasar Sin ta fitar sun nuna cewa, kasar ta fi nuna sha’awar zuba jari a kasashen Afirka. Misali, bisa alkaluman shekara ta 2025, jarin da kasar Sin ta zuba a Afirka ya kai kashi 4.45% na dukkan jarin da ta zuba wa kasashen ketare.
Ban da haka, wani bambanci mai muhimmanci da ya shafi hanyar da kasashen Sin da Amurka suke bi wajen zuba jari a nahiyar Afirka shi ne:A kasar Amurka, wasu manyan kamfanoni ne ke kula da aikin zuba jari a kasuwannin ketare, wadanda ke kokarin neman samun riba daga hawa da sauka na farashin albarkatun kasa a kasuwar duniya. Bisa tantance alkaluma na baya, za mu san cewa, yanayin karuwar jarin da Amurka ta zuba a kasashen Afirka ya samu ne tsakanin shekarar 2005 da ta 2014. A wancan lokacin, hauhawar farashin mai da na wasu danyun kayayyaki ta sa dimbin jari kwarara daga kasar Amurka zuwa sassan sarrafa mai, da iskar gas, da ma’adanai na Afirka. Duk da haka, da zarar farashin albarkatun kasa ya daina hauhawa, to, nan take ake fara samun janyewar jarin kamfanonin Amurka. Alkaluma sun nuna cewa, cikin yawan jarin Amurka da ya ragu a kasuwannin Afirka tsakanin shekarar 2014 da ta 2025, kaso 97% an janye shi ne daga bangaren hakar ma’adinai na kasashen Afirka.
Sabanin yadda kamfanonin Amurka ke son neman samun riba ta hanyar wasu damammaki na bangaren hada-hadar kudi, kamfanonin kasar Sin sun fi son kafa masana’antu, da tsarin sayar da kaya, da na samar da kayayyaki a kasashen Afirka, inda suke neman samun riba ta hanyar gudanar da ayyuka na dogon lokaci. Bugu da kari, jarin da kasar Sin ta zuba a Afirka ya shiga sana’o’i daban daban: daga gina ababen more rayuwa irinsu hanyoyin mota, da layin dogo, da tashoshin jiragen ruwa, da dai sauransu, zuwa ciniki da masana’antu masu alaka da wayoyin salula, da kayayyakin gida, da motoci, har ma da masana’antun zamani masu nasaba da sabon makamashi da fasahar kirkirarriyar basira ta AI, wadanda ke bunkasa cikin matukar sauri a ‘yan shekarun nan, sannan jari daga kasar Sin ya shafi kusan kowane fanni na masana’antu da bangaren sayayya na kasashen Afirka. A ganin kamfanonin kasar Sin, Afirka ba inda ake samun albarkatun kasa kawai ba ce, ita ma babbar kasuwa ce mai tasowa cikin sauri da ke da mutane biliyan 1.4, da ci gaban harkoki daban daban a dimbin biranenta.
Babu shakka, a tsakanin kasashen da ba sa nahiyar Afirka, wadanda manufofinsu suka fi biyan bukatun raya kasa da inganta rayuwar jama’a na kasashen Afirka za su fi samun karbuwa tsakanin ‘yan Afirka. Wannan wani muhimmin dalili ne da ya sa kasar Sin samun karin girmamawa da goyon baya daga ‘yan Afirka a ‘yan shekarun nan. (Bello Wang)













