ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kyamar Baki: Shettima Ya Ja Kunnen Gwamnatin Afirka Ta Kudu

by Rabi'u Ali Indabawa
2 months ago
Baki

Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ya yi kira ga shugabannin kasashen ECOWAS da su hada kai wajen tinkarar yawaitar hare-haren kyamar baki (denophobia) da ake kai wa baki, musamman ‘yan Afirka, a kasar Afirka ta Kudu.

Shettima ya tunatar da gwamnatin Afirka ta Kudu cewa kasashe irin su Nijeriya sun yi gagarumar sadaukarwa wajen tallafa wa gwagwarmayar kawo karshen mulkin wariyar launin fata (Apartheid), har ma ana cire wani bangare na kudaden tallafin karatun daliban Nijeriya domin tallafa wa kungiyoyin neman ‘yancin kai a Kudancin Afirka.

Da yake jawabi a taron karo na 69 na shugabannin kasashen ECOWAS da aka gudanar a Saliyo, Shettima ya bukaci a saka batun hare-haren kyamar baki a cikin ajandar taron na gaba na Kungiyar Tarayyar Afirka (AU).

ADVERTISEMENT

Ya ce akwai bukatar kasashen yankin su fito da murya daya domin dakatar da kara yawaitar nuna kiyayya ga ‘yan Afirka a nahiyar.

A cewarsa, ECOWAS ya kamata ya nuna cewa tashin hankali da nuna wariya ga bakin Afirka ba su da gurbi a nahiyar.

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

Ya ce: “Yayin da muke bin tafarkin sasanci, ya kamata a tunatar da Afirka ta Kudu cewa ‘yancin da take morewa a yau ya samu ne sakamakon gwagwarmayar kasashen Afirka kamar Nijeriya da Ghana.”

Ya kara da cewa: “An rika cire wani bangare na kudaden tallafin karatunmu domin tallafa wa kungiyoyin neman ‘yanci a Kudancin Afirka. Ya kamata su fahimci inda matsalolinsu suke. Matsalarsu ba ta fito daga ‘yan uwansu ‘yan Afirka da suka je kasar domin ba da kwarewarsu ba.”

Jawabin Shettima ya zo ne a daidai lokacin da dangantakar diflomasiyya tsakanin Nijeriya da Afirka ta Kudu ke fuskantar kalubale sakamakon sabon jerin hare-haren kyamar baki da suka yi sanadin mutuwar wasu ‘yan Nijeriya a cikin ‘yan watannin nan.

Nijeriya ta sha yin Allah wadai da kashe ‘yan kasarta tare da neman a yi musu adalci, tana kuma gargadin cewa za ta iya daukar karin matakai idan hare-haren suka ci gaba.

Mataimakin Shugaban Kasar ya jaddada cewa bai kamata a dora wa bakin da ke ba da gudunmawarsu ga tattalin arzikin Afirka ta Kudu laifin matsalolin da kasar ke fuskanta ba.

Ya kuma yi kira ga Kungiyar Tarayyar Afirka (AU) da ta dauki tsayayyen matsayi kan kyamar baki domin kare hakki da lafiyar ‘yan Afirka da ke rayuwa a sassa daban-daban na nahiyar.

Wannan sabon matsayi ya kara nuna yadda Nijeriya ke kara daga murya wajen sukar Afirka ta Kudu tun bayan da hare-haren kyamar baki suka kara kamari a watan Afrilu.

Tun da farko, Ministar Harkokin Wajen Nijeriya, Bianca Odumegwu Ojukwu, ta tunatar da irin rawar da Nijeriya ta taka wajen yaki da mulkin wariyar launin fata a Afirka ta Kudu.

Ta ce: “Nijeriya ta yi sadaukarwa sosai. Ta ba da kudi da sauran kayan tallafi domin taimaka wa Afirka ta Kudu. A makarantu ma, an tanadi guraben karatu ga daliban Afirka ta Kudu. Mu a zamaninmu mun rika daukar allunan zanga-zanga, muna gudanar da zanga-zanga a gaban kadarorin Afirka ta Kudu, har ma wani lokaci ana kama mu saboda hakan.”

Ta kara da cewa ‘yan Nijeriya na matukar takaici da yadda ake mu’amala da bakar fata ‘yan ci-rani a Afirka ta Kudu.

Ta ce: “Ba sa neman sauran bakin kasashen duniya su fita; bakar fata kadai suke son su fice.”

Sabon matsin lambar diflomasiyyar ya biyo bayan wata sabuwar zanga-zangar adawa da baki da ta yi sanadin mutuwar akalla ‘yan Nijeriya hudu.

A martani, Gwamnatin Tarayya ta kwashe ‘yan Nijeriya 1,490 daga Afirka ta Kudu a rukuni bakwai, bayan wasu kungiyoyin kare hakkin dan’Adam sun fitar da wa’adin 30 ga Yuni ga baki da su bar kasar.

Ko da yake Nijeriya ta ci gaba da tattaunawa da Afirka ta Kudu ta hanyar diflomasiyya, ta kuma yi gargadin cewa tana nazarin daukar wasu matakan ramuwar gayya idan aka ci gaba da kai hare-hare kan ‘yan Nijeriya.

Baki
Rabi'u Ali Indabawa
+ postsBio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ƙungiya Ta Gudanar Da Zaɓen Sabbin Shugabanninta A Abuja
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Yadda Tinubu Ya Kashe Naira Biliyan 37.64 A Tafiye-tafiye
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ta’addaci: Mutum 14,500 Sun Bace A Arewa Maso Gabas

MASU ALAKA

'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare
Labarai

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Next Post
Sin Ta Kara Kamfanoni 14 Na Tarayyar Turai Cikin Jerin Wadanda Aka Hana Fitar Masu Da Kaya

Sin Ta Kara Kamfanoni 14 Na Tarayyar Turai Cikin Jerin Wadanda Aka Hana Fitar Masu Da Kaya

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.