ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, July 25, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Jadawalin INEC:Kotun Daukaka Kara Ta Kassara Fatan Jam’iyyu Da ‘Yan Siyasa

by Yusuf Shuaibu
5 hours ago
INEC

Fatan cewa jam’iyyun siyasa za su samu karin lokaci don gudanar da zabukan fitar da gwani kafin zaben 2027 ya rushe a ranar Alhamis bayan da kotun daukar kara ta tabbatar da jaddawalin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) kan tsarin zabe.

Kotun daukar karar da ke zaune a Abuja, ta soke hukuncin babban kotun tarayya na ranar 20 ga Mayu, wanda ya soke wasu bangarorin jaddawalin INEC kuma ya kalubalanci ikon hukumar na kayyade lokacin zabukan cikin gida na jam’iyyun siyasa.

Hukuncin ya dawo da jaddawalin INEC kuma ya rufe kofar kiran a kara wa’adin gudanar da zabukan cikin gida.

ADVERTISEMENT

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa jam’iyyar YP ta kalubalanci halaccin jagororin INEC, tana mai cewa hukumar ba ta da ikon saka gajerar wa’adin daga lokacin da dokar zabe na 2026 ya tanada.

Yawancin jam’iyyun siyasa sun yi fatan cewa karar za ta yi nasara saboda suna ganin ranar 30 ga Mayu ta iyakance musu damar yin amfani da cikakken tsarin dokar zabe, wanda ke ba jam’iyyun har zuwa kwanaki 120 kafin babban zabe don kammala zabukan cikin gida.

LABARAI MASU NASABA

Tinubu Da Atiku Da Obi Na Ci Gaba Da Zafafa Neman Kuri’un Arewacin Nijeriya

Zaben 2027:Tikitin Muslim-muslim Na Jam’iyyar APC Ya Sake Tayar Da Kura

A cikin hukuncin da aka yanke mai alkalai guda uku, kotun daukaka kara ta dauki mataki cewa jam’iyyar YP ba ta da matsayin shari’a don shigar da karar saboda ba ta nuna yadda wadannan ka’idodin suka shafe ta ba.

Kotun ta kara cewa babban kotun tarayya ta yi kuskure wajen tsoma bakin ikon gudanarwar INEC, ta jaddada cewa hukumar ta yi aiki cikin ikon da doka ta ba ta don tsara tsarin zabe.

INEC ta shigar da kara a kotun daukaka kara, tana jayayya cewa babban kotun tarayya ba ta yi la’akari da cikakken ikon shugabanci da dokokin tsarin mulki ya ba ta, kuma karar da jam’iyyar YP ta shigar ba ta da hurumin yin hakan.

Kotun daukaka kara ta bayyana a fili cewa wanda ake karar, jam’iyyar YP ta gaza bayyana yadda jaddawalin INEC ya shafe wajen mika sunayen ‘yan takara.

Lauyen INEC, Aled Izinyon, ya bukaci kotun dauka kara ta soke hukuncin babban kotun tarayya da ta yi kan jaddawalin hukumar zabe domi samun gudanar da zaben 2027 cikin nasara.

Alkalin Adebukola Banjoko, wanda ya jagoranci yanke hukuncin Alkalin Okon Abang ya karanta, ya ce jam’iyyar YP ta kasa nuna yadda jaddawalin suka shafe ta ko mambobinta wajen gudanar da zaben fitar da gwani.

Dukkan alkalai guda uku sun amince gaba daya cewa alkalin babban kotun tarayya, Mohammed Umar, wanda a ranar 20 ga Mayu ya soke jaddawan bisa dalilin cewa sun saba wasu ka’idojin dokar zabe ya yi kuskure wajen soke jaddawan, wanda suka ce wannan hukunci ya haifar da rashin adalci.

Alkali Okon Abang, wanda ya karanta hukuncin kwamitin alkalai guda uku, ya soki kotun farko kan soke ikon gudanarwa na INEC, yana cewa, “Doka ta bai wa INEC ikon gudanar da zabe a kasar.”

“Idan INEC tana aiki cikin ikonta, kotu ba za ta hukumin shiga harkarta. Hukuncin da kotun farko ta bayar kuskure ne, kuma an soke shi a nan.”

Lokacin da aka tuntubi hukumar zabe kan hukuncin, ta yi maraba da hukuncin ranar Alhamis na kotun daukar kara da ya tabbatar da jaddawanta na gudanar da zaben 2027.

A martaninta game da hukuncin, daraktar yada labarai ta hukumar, Bictoria Eta-Messi, ta bayyana hukuncin a matsayin labari mai kyau ga hukumar zabe.

Duk da cewa tuni jam’iyyun siyasa suka kammala zaben fid da gwani na shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya kuma sun gabatar da sunayen ‘yan takararsu ga INEC, masu lura da harkokin siyasa sun ce wani sakamako na daban zai bai wa jam’iyyun karin lokaci don warware rikice-rikicen cikin gida da kuma shari’o’in da ake jira a kotu kafin su kammala mika sunayen ‘yan takara.

Jam’iyyun adawa da dama ciki har da jam’iyyar PDP da ADC suna fama da rikice-rikicen shugabanci da ‘yan takara duk da gudanar da zaben fid da gwani.

Wani bangare na PDP yana goyon bayan tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, a matsayin dan takarar shugaban kasa, yayin da wani bangaren ya gabatar da Sanata Sandy Onor.

Haka zalika, ADC tana ci gaba da samun rarrabun kai tsakanin kwamitin gudanarwa karkashin jagorancin tsohon shugaban majalisar dattawa, Dabid Mark, wanda INEC ta amince da shi kuma ya zabi tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, da kuma wani bangare karkashin jagorancin tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar, Nafiu Bala Gombe, wanda ke ikirarin Chris Uba a matsayin dan takarar shugaban kasa.

Masana sun cewa karin lokaci zai iya bai wa jam’iyyun dama su warware matsalolin da suka shafi nada ‘yan takarar mataimakin shugaban kasa, tun da wasu har yanzu ba su sanar da abokan takararsu ba.

An bayyana cewa ana sa ran hukuncin zai yi tasiri ga zaben fid da gwani na gwamnonin a jihohi, inda bangarori masu hamayya ke ci gaba da ikirarin mallakar tsarin jam’iyya da ‘yan takara.

INEC ta sanya ranar 30 ga Mayu a matsayin ranar kammala zabukan fid da gwani wanda jam’iyyun siyasa suka bi.

Lokacin da aka yanke hukunci a watan Mayu, da yawa daga cikin ‘yan takara masu koke sun yi murna cewa hakan zai ba su karin lokaci don ci gaba da tura bukatunsu.

Sakataren yada labarai na jam’iyyar NDC, Osa Director, bai amsa kiran wayar da aka yi masa jiya don jin ra’ayin jam’iyyar kan hukuncin ba.

Sai dai wani jigon jam’iyyar, wanda ya nemi a boye sunansa, ya ce hukuncin kotun daukaka kara bai shafi jam’iyyar ta kowace hanya ba.

Shi ma sakataren yada labarai na jam’iyyar PDP da bangaren Kabiru Turaki ke jagoranta, Ini Ememobong, ya ce za su yi magana kan wannan ci gaba bayan zaman kotu kan batu a yau.

Jam’iyyar PRP ta bayyana cewa hukuncin da kotun ta yanke ranar Alhamis, wanda ya tabbatar da jaddawalin INEC na gudanar da zabukan 2027, bai shafi jam’iyyarsu ba.

INEC
Yusuf Shuaibu
+ postsBio
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    Tinubu Da Atiku Da Obi Na Ci Gaba Da Zafafa Neman Kuri’un Arewacin Nijeriya
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    Zaben 2027:Tikitin Muslim-muslim Na Jam’iyyar APC Ya Sake Tayar Da Kura
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    Amurka Ta Yi Alƙawarin Sa Ido Sosai A Zaɓen Nijeriya Na 2027
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    Sautin Muryar Da Aka Fallasa Kan El-Rufai Ya Haifar Da Zazzafar Muhawara

MASU ALAKA

Tinubu Da Atiku Da Obi Na Ci Gaba Da Zafafa Neman Kuri’un Arewacin Nijeriya
Tambarin Dimokuradiyya

Tinubu Da Atiku Da Obi Na Ci Gaba Da Zafafa Neman Kuri’un Arewacin Nijeriya

July 17, 2026
Zaben 2027:Tikitin Muslim-muslim Na Jam’iyyar APC Ya Sake Tayar Da Kura
Tambarin Dimokuradiyya

Zaben 2027:Tikitin Muslim-muslim Na Jam’iyyar APC Ya Sake Tayar Da Kura

July 17, 2026
‘Yan Ƙasar Turkiyya Sun Nuna Jarumta Da Kare Dimokuraɗiyya Mafi Girma A Tarihi – Erdoğan
Manyan Labarai

‘Yan Ƙasar Turkiyya Sun Nuna Jarumta Da Kare Dimokuraɗiyya Mafi Girma A Tarihi – Erdoğan

July 15, 2026
Next Post
Ta Da Zaune Tsaye Da Philippines Ta Yi A Teku Ba Zai Lalata Dangantakar Hadin Gwiwar Sin Da ASEAN Ba

Ta Da Zaune Tsaye Da Philippines Ta Yi A Teku Ba Zai Lalata Dangantakar Hadin Gwiwar Sin Da ASEAN Ba

LABARAI MASU NASABA

An Karrama Masana Ilimin Lissafi Na Kasar Sin Da Lambobin Yabo Na Fields Medal

An Karrama Masana Ilimin Lissafi Na Kasar Sin Da Lambobin Yabo Na Fields Medal

July 24, 2026
Ta Da Zaune Tsaye Da Philippines Ta Yi A Teku Ba Zai Lalata Dangantakar Hadin Gwiwar Sin Da ASEAN Ba

Ta Da Zaune Tsaye Da Philippines Ta Yi A Teku Ba Zai Lalata Dangantakar Hadin Gwiwar Sin Da ASEAN Ba

July 24, 2026
Jadawalin INEC:Kotun Daukaka Kara Ta Kassara Fatan Jam’iyyu Da ‘Yan Siyasa

Jadawalin INEC:Kotun Daukaka Kara Ta Kassara Fatan Jam’iyyu Da ‘Yan Siyasa

July 24, 2026
An Zartas Da Sanarwar Chengdu A Taron Ministocin Kungiyar APEC Kan Harkar Raya Fasahohin Dijital Da AI

An Zartas Da Sanarwar Chengdu A Taron Ministocin Kungiyar APEC Kan Harkar Raya Fasahohin Dijital Da AI

July 24, 2026
NNPP Za Ta Kwace Mulki A Jihar Imo – Kwankwaso

Jam’iyyar NDC Ta Shirya Tsaf Domin Kafa Gwamnati A 2027 —Kwankwaso

July 24, 2026
Sin Ta Kara Kamfanoni 14 Na Tarayyar Turai Cikin Jerin Wadanda Aka Hana Fitar Masu Da Kaya

Sin Ta Kara Kamfanoni 14 Na Tarayyar Turai Cikin Jerin Wadanda Aka Hana Fitar Masu Da Kaya

July 24, 2026
Kashim Shettima Ya Mayar Da Martani Kan Tsadar Rayuwa

Kyamar Baki: Shettima Ya Ja Kunnen Gwamnatin Afirka Ta Kudu

July 24, 2026
Yadda Kasar Sin Ta Samar Da Ci Gaba Na Bai Daya

Yadda Kasar Sin Ta Samar Da Ci Gaba Na Bai Daya

July 24, 2026
Hatsin Da Kasar Sin Ta Girbe Da Lokacin Zafin Bana Ya Zarce Tan Miliyan 150

Hatsin Da Kasar Sin Ta Girbe Da Lokacin Zafin Bana Ya Zarce Tan Miliyan 150

July 24, 2026
Wani Dalilin Da Ya Sa Al’Ummar Afirka Ke Kaunar Kasar Sin Shi Ne Yadda Take Kokarin Zuba Musu Jari

Wani Dalilin Da Ya Sa Al’Ummar Afirka Ke Kaunar Kasar Sin Shi Ne Yadda Take Kokarin Zuba Musu Jari

July 24, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.