Lamarin gibi ta fuskar ci gaba tsakanin gabashin da yammacin Sin wani batu ne da ake yawan tattauna a kansa da nufin gano yadda za a cike wannan gibi. Shi dai yankin na gabashin Sin, wanda yake gabar ruwa, yana da kyakkyawan tsarin sufuri, sannan kuma yana kusa da tashar jiragen ruwa, abin da ya baiwa yankin damar kasuwanci da sauran kasashen duniya. A waje daya kuma yankin na yammaci Sin yanki ne da za a iya cewa yana kurya, amma kuma Allah ya albarkaci yankin da filin noma, da jama’a, da kuma albarkatun kasa, ko da yake ma’amalar kasuwanci da sauran kasashen duniya abu ne mai matukar wuya. Wannan yanayi shi ne ya sanya yankin na gabashi ya baiwa yanki na yammaci tazara sosai ta fannin ci gaban tattalin arziki.
A watan Yulin shekara ta 2016 ne, shugaban kasar Sin Xi jinping ya jagoranci wani taron tattaunawa a garin Yinchuan dake jihar Ningxia ta arewa maso yammacin kasar, kan hadin gwiwa tsakanin lardunan gabashi da na yammaci da nufin lalubo bakin zare kan yadda za a fitar da larduna na yammaci daga cikin kangin talauci.Yau shekaru goma ke nan da suka shude da gudanar da wannan taron tattaunawa, sai ga shi wannan mataki ya haifar da kyakkyawan sakamako. Matakin bai tsaya ga batun kawar da talauci ba kadai, ya fadada ya zuwa samar da bunkasuwar tattalin arzikin yankin, tare da daga matsayin yankunan karkara daga matakin talauci ya zuwa matakin wadata da bunkasuwar zaman takewa.
Domin cike wannan wagegen gibi ta fuskar ci gaban tattalin arziki, yankunan biyu sun hada karfi da karfe wajen yakar talauci da koma bayan tattalin arziki. Yayin da lardunan na gabashi suka samar da kudade, fasaha, kwararru da kuma kasuwanni, su kuma larduna na yammaci suka yi amfani da albarkar filayen noma, dimbin ’yan kwadago da kuma albarkatun kasa wajen hada karfi da karfe domin cimma wannan burin a yaki da talauci da koma baya a larduna na yammaci.
Wannan tsari na hadin gwiwa ya taka muhimmiyar rawa wajen dakile talauci. Domin kuwa alkaluma sun nuna cewa a karshen shekara ta 2020, daukacin al’ummomin da ke fama da talauci da yawansu ya kai kusan miliyan 98.99, sun samu nasarar ficewa daga cikin kangin talauci, yayin da daukacin gundumomi 832 aka cire su daga cikin jerin sunayen gundumomin dake fama da talauci. Haka nan kuma illahirin kauyuka dubu 128 suka samu waraka daga kangin talauci da koma baya.
A takaice dai za’a iya cewa, wannan yanki na yammaci ya samu nasarar ficewa daga kangin talauci da koma bayan tattalin arziki. Yawan kudaden shiga na iyalai a yankunan karkara ya yi matukar karuwa, kuma yana ci gaba da bunkasa. Jimillar karuwar kudaden shiga daga kauyukan da aka fitar daga kangin talauci ya taimaka wajen bunkasuwar tattalin arzikin lardin na yammacin Sin tare da taimakawa wajen cike babban gibin dake akwai tsakanin lardunan biyu.
Shi dai wannan tsari na hadin gwiwa tsakanin gabashi da yammaci tsari ne wanda gwamnati, ’yan kasuwa da hukumomi suka hada karfi da karfe domin cimma buri na bai daya, wato kawar da talauci a yankin na yammaci, abin da kuma ya haifar da ci gaba da bunkasuwar tattalin arzikin yankin baki daya.














