ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, July 25, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tsakanin Digiri Da Sana’a Wanne Ya Fi Muhimmanci A Wannan Lokacin?

by Muhammad Bakir Bello
1 hour ago
Digiri

A wannan makon ma, masu karatu sun bayyana mana ra’ayoyinsu, kan tsakanin digiri da sana’a, wanne ne ya fi muhimmanci, musamman a wannan lokaci na matsalar tattalin arziki da ake fama da shi.  Kamar kullum Sani Anwar da Muhammad Bakir Bello suka tattara mana.

Zainab Abdullahi Sarki, daga Zaria Jihar Kaduna

A ganina, ba za a ce digiri ya fi sana’a muhimmanci, ko kuma sana’a ta fi digiri a kowane hali ba. Digiri yana bai wa mutum ilimi mai zurfi da damar samun ayyuka a hukumomi da manyan kamfanoni, yayin da sana’a kuma ke bai wa mutum kwarewar da zai iya dogaro da ita, wajen samun kudin shiga da kuma zama mai cin gashin kansa.

ADVERTISEMENT

A wannan zamani, hada digiri da sana’a shi ne mafi alheri. Mutum mai digiri da kuma kwarewar sana’a, yana da fa’ida fiye da wanda yake da daya kawai. Idan aiki bai samu ba, sana’a za ta taimaka masa ya ci gaba da dogaro da kansa, sannan digiri zai kara bude masa karin damammaki a nan gaba.

Muhimman abubuwa:  Digiri yana bude damar samun ayyukan kwararru. Sana’a tana ba mutum hanyar samun kudin shiga cikin sauri. Sana’a tana karfafa dogaro da kai. Hada digiri da sana’a shi ne mafi kyawun zabi. Ilimi da kwarewa idan sun hadu, suna kara damar samun nasara.

LABARAI MASU NASABA

Tasirin AI (Artificial Intelligence) A Harkokin Al’umma Na Yau Da Kullum

Ra’ayin Al’umma Game Da Shirin Gwamnati Na Sake Fasalin Hukumar NYSC

Zainab Mika’il, daga Zaria Jihar Kaduna

Sana’a da digiri duka suna da muhimmanci a rayuwar Dan’adam, domin suna taimakawa wajen samun ilimi da kuma hanyoyin samun kudin shiga. Duk da haka, mutane da dama suna ganin cewa; sana’a ta fi digiri amfani a wasu fannonin, saboda tana ba mutum damar dogaro da kansa cikin sauri.

Na farko, sana’a tana taimaka wa mutum ya fara samun kudin shiga cikin gaggawa. Bayan koyon sana’a, mutum zai iya fara aiki ko kuma ya bude nasa kasuwancin ba tare da ya jira samun aikin gwamnati ko na kamfani ba.

Na biyu, sana’a tana rage zaman banza da rashin aikin yi. A yau, akwai masu digiri da yawa da ba su samu aikin yi ba, amma mai sana’a na iya amfani da kwarewarsa wajen samar wa kansa abin dogaro.

Na uku, sana’a tana ƙarfafa tattalin arziki. Idan mutane da yawa suna da sana’o’i, za su samar da kayayyaki da ayyuka, su kuma ɗauki wasu ma’aikata aiki. Wannan yana taimakawa wajen rage talauci da bunƙasa tattalin arzikin ƙasa.

 Ahmad Bello, daga Jami’ar ABU Zaria Jihar Kaduna

Duka suna da amfani, amma zance na gaskiya digiri ya fi muhimmanci. Saboda ilimi shi ne jigon rayuwa. Duk abin da za ka yi, indai da ilimi, za ka ga ya yi banban da na wanda ba shi da ilimi. Ko sana’a idan mutum zai yi ba da ilimi ba za ka ga ba ta kai na wanda ke da digiri ba.

Adam Bello Hamza

Digiri ko sana’a? A Nijeriya, sana’a na kawo kudi cikin sauri, digiri kuma na bude manyan damammaki. wanda ya fi muhimmanci shi ne abin da zai ba ka halal, kwarewa, da ‘yancin dogaro da kai. Idan ka hada su, shi ne mafi alheri.  Don a ra’ayina babu wanda ya fi daya muhimmanci kai tsaye.

Aisha Usman, daga Maiduguri Jihar Borno

A nawa ra’ayin dukkansu suna da matukar muhimmanci, saboda haka ya kamata mutum ya yi kokari ya hada duka biyun. Ma’ana ya kamata mutum ya tabbatar da ya kama wata sana’ar da zai dogara da ita, ko da kuwa yana karatun boko ne a jami’a, domin a wannan zamanin babu tabbas a wajen samun aikin gwamnati a cikin sauri, ka ga sai mutum ya samu abin da zai rike kansa kafin ya samu hanyoyin kudin shiga. Ni dai ina karatun boko, kuma ina da sana’ar hannu. Na gode.

Sunana Usman Sani Amar, daga Abuja

A wannan lokacin, babu wanda ya fi wani muhimmanci gaba-daya. Digiri na bude kofofin samun aiki da ci gaba a fannoni da dama, yayin da sana’a ke bai wa mutum damar dogaro da kansa da samun kudaden shiga cikin gaggawa. A Nijeriya ta yau, inda rashin aikin yi ya yi yawa, mutane da yawa suna hada ilimi da sana’a, domin kara samun dama.

Saboda haka, abin da ya fi muhimmanci shi ne, mutum ya kasance yana da kwarewar da ake bukata a kasuwa. Idan kana da digiri ka rasa kwarewa, ko kuma kana da sana’a ba tare da ci gaba da koyon sabbin dabaru ba, za ka iya fuskantar kalubale. A yau, hada digiri da sana’a shi ne mafi kyawun hanyar samun nasara.

 Sunana Habiba, daga Kano

A ganina, ba daidai ba ne a ce digiri ya fi sana’a muhimmanci, ko kuma sana’a ta fi digiri muhimmanci. Kowannensu yana da rawar da yake takawa wajen ci gaban mutum da al’umma. A wannan zamani, abin da ya fi dacewa shi ne, hada ilimin boko da kwarewar sana’a.

Digiri yana bai wa mutum ilimi mai zurfi, yana gina tunani, kuma yana bude kofofin shiga fannoni kamar koyarwa, lafiya, shari’a, injiniya, da sauran ayyukan da ke bukatar kwararru.

Haka kuma, yana kara wa mutum kima da damar ci gaba da karatu zuwa manyan matakai.

A gefe guda kuma, sana’a tana bai wa mutum damar dogaro da kai da samun abin yi cikin gaggawa. A halin da ake ciki na kalubalen tattalin arziki da karancin ayyukan yi, sana’a ta zama hanya mai muhimmanci wajen rage zaman banza, samar da aikin yi da bunkasa tattalin arzikin kasa.

Bilkisu Maharazu, daga Jihar Katsina

A wannan zamani da muke ciki, ina ganin sana’a ta fi digiri muhimmanci, ba don digiri ba shi da nasa amfanin ba, amma saboda yanayin rayuwa da tattalin arziki sun canza. Digiri na ba mutum ilimi da takardar shaidar karatu, amma ba koyaushe yake tabbatar da samun aiki ko samun kudin shiga ba. A yau akwai dubban masu digiri da suke zaman jiran aiki na tsawon shekaru saboda karancin guraben aiki, yayin da mutane masu sana’a ke samun damar dogaro da kansu da kuma

Digiri
Muhammad Bakir Bello
+ postsBio
    This author does not have any more posts.

MASU ALAKA

Tasirin AI (Artificial Intelligence) A Harkokin Al’umma Na Yau Da Kullum
Taskira

Tasirin AI (Artificial Intelligence) A Harkokin Al’umma Na Yau Da Kullum

July 18, 2026
Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya
Taskira

Ra’ayin Al’umma Game Da Shirin Gwamnati Na Sake Fasalin Hukumar NYSC

July 11, 2026
Ko Kafa Ƴansandan Jihohi Zai Taimaka Wajen Kawo Ƙarshen Matsalolin Tsaro?
Taskira

Ko Kafa Ƴansandan Jihohi Zai Taimaka Wajen Kawo Ƙarshen Matsalolin Tsaro?

July 5, 2026
Next Post
Wane Ne Khalil Al-Hayya, Sabon Shugaban Kungiyar Hamas?

Wane Ne Khalil Al-Hayya, Sabon Shugaban Kungiyar Hamas?

LABARAI MASU NASABA

Wane Ne Khalil Al-Hayya, Sabon Shugaban Kungiyar Hamas?

Wane Ne Khalil Al-Hayya, Sabon Shugaban Kungiyar Hamas?

July 25, 2026
Tsakanin Digiri Da Sana’a Wanne Ya Fi Muhimmanci A Wannan Lokacin?

Tsakanin Digiri Da Sana’a Wanne Ya Fi Muhimmanci A Wannan Lokacin?

July 25, 2026
Digiri

Sojoji Sun Kamata Ƴan Bindiga 5 Da Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane A Yobe

July 25, 2026
Gwamnatin Jihar Kano Za Ta Fara Aiwatar Da Shirin Inshorar Lafiya Ga Jaruman Kannywood

Gwamnatin Jihar Kano Za Ta Fara Aiwatar Da Shirin Inshorar Lafiya Ga Jaruman Kannywood

July 25, 2026
Digiri

Ku Buɗe Wuta Kan Duk Wanda Kuka Gani Ɗauke Da Bindiga – IGP

July 25, 2026
Idan Aka Cire Bangaren Man Fetur Kannywood Ce Ta Fi Samar Da Aikin Yi Ga Matasa —Hamisu Iyantama

Idan Aka Cire Bangaren Man Fetur Kannywood Ce Ta Fi Samar Da Aikin Yi Ga Matasa —Hamisu Iyantama

July 25, 2026
Kogin Kumadugu Ya Yi Ambaliya Karon Farko Cikin Shekara 100 A Yobe

Jihohi 28 Da Abuja Na Fuskantar Hadarin Ambaliyar Ruwa —Rahoto

July 25, 2026
Digiri

Ƴan Bindiga Sun Sace Shugaban Ƙaramar Hukumar Bungudu

July 25, 2026
Yadda Jami’an Tsaro Suka Fatattaki ’Yan Ta’adda A Wasu Jihohin Nijeriya, Sun Kama ‘Yan Kasar Pakistan Bakwai

Yadda Jami’an Tsaro Suka Fatattaki ’Yan Ta’adda A Wasu Jihohin Nijeriya, Sun Kama ‘Yan Kasar Pakistan Bakwai

July 25, 2026
Digiri

Obasanjo Da Atiku Sun Sake Musayar Zafafan Kalaman Zargin Juna

July 25, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.