Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home Waiwayen Kanun Labarai

Waiwayen Kanun Labaru: Daga Litinin 3 Zuwa Alhamis 6 Ga Rajab 1442 Bayan Hijira  

by Muhammad
February 19, 2021
in Waiwayen Kanun Labarai
7 min read
Labaru
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

LITININ

Jama’a na ci gaba da korafin gidan talabijin na TBC, da Channels, da AIT, da ARISE da sauransu, da yake nasu ne, ba su mayar da hankali ga ba da rahoton abin da yarbawa suka yi wa Hausawa a Kasuwar Sasa ba. Ana ta korafin da a ce Hausawa ko Fulani ne suka yi wa Yarbawa haka a nan Arewa ko a can yankin, da yanzun sun dau dumi suna ta sa rahoton da sharhi iri-iri kai ka ce tashin duniya ne. Masu korafin suka ce da yanzun kungiyoyinsu da lauyoyinsu, da ‘yan bokonsu, sun tasa Hausawa da Fulani a gaba ba sararawa.

samndaads

Mataimakin Shugaban Kasa Osinbanjo ya yi kiran a zauna lafiya a tsakanin ‘yan kasuwa Hausawa da Yarbawa da ke Ibadan. Haka nan gwamnan jihar Oyo da na jihar Ondo sun ziyarci kasuwar da aka yi wa Hausawa barna, da kisa, da kona musu motoci da muhalli, da rumfuna. Rahotanni na nuna duk da an sa dokar hana walwala, Yarbawa sun ci gaba da kai wa Hausawa hari da lalata musu dukiya. A yanzun haka dubban Hausawa sun fake suna gudun hijira a gidan Sarkin Hausawa.

Wasu na ci gaba da kiran tunda auren tsakanin Kudu da Arewa ya gagara, a raba mana kowa ya san inda dare ya masa.

Wani rahoto na nuna kidinafas sun tare wata motar daukar fasinja ta hukumar sufuri ta jihar Neja, a karamar hukumar Rafi, ta fito daga Kwantagora za ta Minna, suka yi kidinafin fasinjoji 18 da ke ciki, suka kyale wata mai goyo da goyon nata, ba su tafi da ita ba.

Sojoji sun ce sun kashe wasu manyan kwamandojin Shekau su biyu, da suke nema ruwa a jallo, Abdul-Bas da Ibn Habib.

Mai ba da shawara bangaren tsaro na kasa, da sabbin hafsoshin tsaro, da gwamnonin Arewa maso yammacin kasar nan, za su yi taro a Kaduna, don gano bakin zaren magance matsalar tsaro da ke addabar yankin.

A shekarar 2020 kwamitin nan mai kaso da raba kudade duk wata ga gwamnatin tarayya, da jihohi da kananan hukumomi FAAC, ya ce ya hankada musu naira tiriliyan biyar ba wasu ‘yan canji, 4.75trn.

Af!

Ga wani rubutu da na yi ranar 14 ga watan Fabrairu na shekarar 2016, wato shekara biyar ke nan.

“Ni dai daga daya ga watan nan na Fabrairu da aka kara kudin wuta babu wata inganta da wutar ta yi sai ma kara tabarbarewa da ta yi. Wannan zalunci har ina? Akwai ministoci biyu da nake so Baba Buhari ya sauke su don ba su da amfani kuma suna yi wa gwamnatin Buhari zagon kasa. Ministan lantarki da karamin ministan mai. Gaskiya su tarkata inasu-inasu su san inda dare ya musu tun rana ba ta fadi ba”

 

 

TALATA

Labarin da ya fi farin jini ranar Litinin shi ne zabar Dafta Ngozi Okonjo-Iweala a matsayin Babbar Shugabar Cibiyar Hada-hadar Kasuwanci ta Duniya wato WTO a takaice. Mace ta farko da aka taba zaba a wannan mukami, ‘yar Afirka ta farko, ‘yar Nijeriya ta farko. Da ma tana ta yin ta farko a abubuwa, misali ita ce ministar kudi ta farko mace, ta yi a zamanin Obasanjo, aka kuma nada ta a gwamnatin Jonathan, wacce ita ce mace ta farko kuma ministar kudi da ta taba samun haka. Shugaban Kasa Buhari, da Shugabannin Majalisun Dokoki su Ahmed Lawan da Gbajabiamila sun nuna farin cikinsu da zabarta.

Shugaban ‘yan sandan Nijeriya, ya tura wasu dakarun ‘yan sanda na musamman da ake kira da INTERBENTION AND STABLIZATION FORCES, Kasuwar Sasa ta jihar Oyo da Yarbawa suka yi wa Hausawa rotse don dauki da daidaita lamura.

Gwamnonin jihohin Arewa hudu, na Zamfara, da na Kabbi, da na Kano, da Neja, sun yi wa gwamnan jihar Oyo Makinde takakkiya har jihar, su ji dalilin da ya sa Yarbawa ke yawan yi wa Hausawa da ke can rotse.

Gwamnonin jihohin Arewa Maso Yamma, sun yo takakkiya zuwa nan Kaduna, inda suka yi taro da hafsoshin tsaro, da mai ba shugaban kasa shawara bangaren tsaro, don yi wa matsalar tsaro da ke addabar yankin taron dangi, su yi koli-koli da ita, su tandara da kasa, sai dai kashi! Sun ce sun so su yi tuya su manta albasa, ba sarakuna ba malamai, saboda haka, kowa ya mayar da akayau dinsa, sai an kara shiri.

Wasu ‘yan bindiga sun kashe mutum uku, da kona gidaje a jihar Filato.

Za a gudanar da zaben kananan hukumomi na jihar Kaduna a ranar Asabar 15 ga watan Mayu na wannan shekara.

Af:

Da karfe hudun asubah ta gota da wajen minti goma, sai in ga mutane na ta kiran wayata, wai ba su ga na sako labaru ba. Sai in ta ba su hakuri cewa ina kan rubutawa ne.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya aike wa Majalisar Dattawa sunan Abdulrasheed Bawa don ta amince masa nadin da ya masa a matsayin sabon shugaban hukumar EFCC.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya hori sabbin jakadun da ya nada, su yi kokarin kare martabar kasar nan, da kimarta a can kasashen da za a tura su huldar jakadanci.

Majalisar Wakilai ta bukaci shugaban ‘yan sandan Nijeriya, ya hanzarta gudanar da binciken kisan da Yarbawa suka yi wa Hausawa da da lalata musu dukiya a Sasa da ke Ibadan a jihar Oyo.

Gwamnonin nan hudu, da suka yi takakkiya zuwa jihar Oyo wajen Makinde, na Neja, da Zamfara, da Kano da Kabbi, sun leka har kasuwar ta Sasa inda Yarbawa suka yi wa Hausawa aika-aika.

Af!

An ja hankalina zuwa ga wata fosta a fesbuk ta yakin neman zabe a karamar hukumar Kudan, inda aka nuna wata gada, cewa ta Guibi ce aka gyara. Ina gani na kira mutanen Guibi a waya, na tambaye su an gyara gadar ne? Suka ce ba a gyara ba. To ya kamata mutanen Guibi su ankara cewa, ana nan ana yakin neman zabe da wata gada, cewa gadarsu ce aka gyara.

 

ALHAMIS

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da kidinafin mutane 42 a makarantar sakandare ta kimiyya da ke Kagara jihar Neja. Tare da tura dakaru na musamman don ceto su ba tare da an yi wa wani kwarzane ba.

Majalisar Dattawa ta ce ba Allah wadai ko tir Shugaban Kasa zai tsaya kullum yana yi ba, lokaci ya yi da zai sa wa bangaren tsaro dokar ta bacci.

Ministan tsaro Bashir Magashi, ya bai wa ‘yan Nijeriya shawarar idan kidinafas, ko makasa, ko ‘yan fashin daji sun kai musu farmaki, su daina zama suna kallo kamar yadda ya fada da turanci NOT TO BE COWARDS. Jama’a su dinga mikewa suna tabukawa don kare kansu.

Kwamitin tsaro na hadin gwiwa na Majalisar Dokoki ta Tarayya, bangaren sojan kasa, da na sama, da na ruwa, ya soma tantance sabbin hafsoshin tsaro da shugaban kasa ya nada.

Kungiyar Gwamnonin Nijeriya,  gwamnan jihar Kano, da na Edo, da na Oyo, da na Ekiti, da na Neja, da na Sakkwato, da na Bauci, da na Imo, sun gudanar da wani taro a Fadar Shugaban Kasa, inda cikin abubuwan da suka cimma, har da yin tsayin daka wajen kare rayukan jama’a da ke jihohinsu.

Biyo bayan kidinafin ‘yan makarantar Kagara, Gwamnan jihar Neja Bello, ya rufe wasu makarantun kwana da ke yankunan da kidinafas suka fi matsawa. Ya kuma ce ba zai biya ko taro kudin fansa ba.

Gwamnonin PDP sun ce hanya daya da za a bi don shawo kan matsalar tsaro, ita ce iko da ‘yan sanda, ya dawo hannun hukumomi na kasa, ba kacokan a hannun tarayya, wato can sama kamar yadda ake yanzun da gwamnan jiha ba shi da iko da su ba.Gwamnonin sun kuma bukaci ko dai a nada shugaban ‘yan sanda mai riko, ko ba mai riko ba, a kyale Mohammed Adamu da ya kamata a ce ya yi ritaya ya san inda dare ya masa.

A jihar Yobe ‘yan Boko Haram sun kashe wasu ‘yan sandan kwantar da tarzoma su hudu.

A jihar Kaduna, bayan kidinafin Sarkin Rimau da ke gabas da Kasuwar Magani shekaranjiya waccar, a yanzun sun shiga Kasuwar Magani sun yi kidinafin wasu mutane har da mace. Sannan a yankin Birnin Gwari, har sun kwashi mutum hudu, sojoji suka musu kofar rago, suka ceto mutanen, suka kashe da dama daga cikinsu, wasunsu suka tsere da raunin harbin bindiga. Har suka bar bindiga kirar AK47.

Ministan Lantarki ya ce duk wata sai gwamnati ta tallafa da kudi naira biliyan hamsin na wutar lantarki da jama’a ke sha.

Jama’a na ci gaba da korafin, ba a ba su wutar naira dubu uku a wata, amma ana tilasta musu biyan naira dubu talatin a watan, da ke nuna ana damfarar talaka naira dubu ashirin da bakwai duk wata.

Kamfanin mai na kasa NNPC ya ce babu wani yunkuri na yin karin kudin mai a yanzun.

Hukumar ICPC, ta ce ta gano wata naira biliyan 42, da wasu hukumomin lafiya, da cibjyoyin ilimi da ba su kashe su ba, da in aka yi sake wasu gafiyoyi za su yi ta kansu. Saboda haka ta yi wa kudaden kofar rago.

Bankin ba da lamani na duniya IMF, ya goyi bayan haramta kudin CRYPTO/ KIRIFTO da Babban Bankin Nijeriya ya yi.

Bayanan sun nuna rabon da kayayyaki su yi tsada wato INFLATION irin yadda suka yi yanzun, tun shekarar 2016.

Ana ci gaba da ankarar da mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, cewa ‘yan siyasar karamar hukumar da ke neman tazarce, na amfani da hoton wata gada, cewa gadar Guibi ce aka gyara, alhali gadar na nan ba a gyarata ba.

Ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i duk na Gwamnatin Tarayya, na ci gaba da korafin watan jibi za su cika shekara biyu suna dakon ariyas na sabon albashi.

 

SendShareTweetShare
Previous Post

Bai’atur Ridwan: Sahabban Da Suka Yi Mubaya’a Da Manzon Allah Sun Yi Da Allah Ne (II)

Next Post

‘Yan Nijeriya Miliyan 30 Ke Samun Tabin Hankali Sakamakon Shaye-shaye – Dakta Nafisa

RelatedPosts

Waiwayen Kanun Labaru: Daga Litinin 25 Zuwa Alhamis 28 Ga Jimada Sani 1442 Bayan Hijira

Waiwayen Kanun Labaru: Daga Litinin 25 Zuwa Alhamis 28 Ga Jimada Sani 1442 Bayan Hijira

by Sulaiman Ibrahim
2 weeks ago
0

LITININ Gwamnatin jihar Kogi ta yi barazanar za ta garzaya...

Labaru

Waiwayen Kanun Labaru: Daga Lahadi 17 Zuwa Alhamis 21 Ga Jimada Sani 1442, Bayan Hijira

by Muhammad
3 weeks ago
0

LAHADI Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya samu sabon dogari Kanal...

Waiwayen Kanun Labaru: Daga Lahadi 10 Zuwa 13 Ga Jimada Sani 1442, Bayan Hijira

Waiwayen Kanun Labaru: Daga Lahadi 10 Zuwa 13 Ga Jimada Sani 1442, Bayan Hijira

by Sulaiman Ibrahim
4 weeks ago
0

Lahadi Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya halarci wani taro na...

Next Post
Shaye-shaye

‘Yan Nijeriya Miliyan 30 Ke Samun Tabin Hankali Sakamakon Shaye-shaye - Dakta Nafisa

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version