ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, December 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Wajibcin Azumi

by Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
10 months ago
Azumi

Alhamdu lillah. Masu karatu barkan mu da sake haduwa a ci gaba da darasinmu na Azumin watan Ramadan.

Kamar yadda darasinmu na makon da ya gabata y afara bayani a kai, lallai azumin Ramadan wajibi ne ga dukkan Musulmi baligi mai lafiya ba mara lafiya ba, wajibcin azumi kamar yadda Allah ya fada a cikin Al’kur’ani da fadarsa yana cewa: “Ya ku Muminai Allah Ya wajabta muku yin azumi kamar yadda ya wajabta ma wadanda suka zo kafin ku, ko za ku ji tsoron Ubangijinku. Kwanaki ne kididdigaggu, wanda ya kasance a cikinku bai da lafiya ko kuma yana kan tafiya, to ya rama abin da ya kubuce masa a wasu ranakun, wadanda kuma ba za su iya yin azumin ba, to su ciyar da Miskinai, amma wanda yake da damar ciyar da miskinai da yawa, to ya yi alkairi ne a wajenshi, lallai yin azumin ya fi alkairi a gare ku, idan kun san wannan alkairin da ke cikin azumin.”

  • Hakuri Da Baiwa (Kyautar) Manzon Allah (SAW)
  • Wasu Ruwayoyi Game Da Yafiyar Manzon Allah (SAW)

Abdulrahman bin Auf, ya ce, Manzon Allah (SAW) ya ce “Innallaha farada siyamu ramadana alaikum, wa sanantu lakum kiyamuhu, faman samahu wa kamahu imanan wahtisaban, kharaja min zunubihi ka yaumi waladat’hu Ummuhu – Allah ya farlanta muku yin Azumin watan Ramadana, ni kuma na sunnanta muku yin Sallollin tarawihi na dare a cikinshi, duk wanda ya azumce shi kuma ya yi ibada a cikinshi don Imani da neman leda, zai fita daga cikin watan Ramadana an yafe mishi zunubansa kamar yadda mahaifiyarshi ta haife shi.” Ya zama kamar sabon haihuwa bai da zunubi ko kadan.

ADVERTISEMENT

Azumi ya wajaba kan Musulmi, Da ba bawa ba, baligi mai lafiya, amma ba laifi a dinga koya wa yara yin azumin. Mara lafiya da Matafiyi da mai Haila da mai Jinin biki za su rama azumin da ya kubuce musu. Amma tsoho wanda ba zai iya azumtar azumin ba da fursuna da aka yanke wa hukuncin zaman gidan yari har abada sannan kuma akwai aiki mai wuya da aka dora masa kullum, su wadannan azumi ya fadi a kansu. In suna da hali, su dinga ciyarwa.

Mace mai Juna-biyu da mai Shayarwa, su rama azumin in za su iya ko su ciyar.

LABARAI MASU NASABA

Annabi SAW Ya Zarce Duk Sauran Annabawa Yawan Mu’uzijoji

Allah Ya Bai Wa Annabi (SAW) Mu’ujizozi Fiye Da 2,000 A Alƙur’ani  

 

Jinkirta Sahur Da Gaggauta Buda-baki

An karba daga Anas, ya ce, Annabi SAW ya ce “ku dinga yin Sahur, domin shi yin Sahur akwai albarka a cikinsa”, ba burgewa ba ce mutum ya dinga cewa ‘ai ni ban yin sahur’ albarka mai yawa ta wuce shi.

An karba daga Sahlu dan Sa’adu Allah ya kara yarda da shi ya ce, Manzon Allah (SAW) ya ce “Mutane ba za su gushe ba cikin alkairi muddin sun gaggauta yin buda-baki” Ma’anar wannan hadisi, sabida Allah ya fada cikin Alkur’ani “summa atimmus siyama ilallai – sannan ku cika azumi zuwa dare” sai Annabi ya koya mana sunnarshi zuwa dai-dai lokacin da ya dace na buda-bakin (ba cikin dare Allah yake nufi ba), sai Annabi SAW ya bayyana da fadarsa ku gaggauta yin buda baki – da rana ta fadi, an sha ruwa.

Manzon Allah (SAW) ya kasance in an sha ruwa yana fara bude baki ne da addu’a inda yake cewa “Allahumma laka sumtu wa ala rizkika afdartu – Ya Allah a gareka nake Azumi kuma cikin arzikinka nake buda-baki” mai azumi cikin hadarar Allah yake don haka a wurin mai arziki mai azumi yake shan ruwa.

An karba daga Abi Zaidil Gifari ya daga hadisin zuwa ga Annabi SAW yace “Ma zala Ummati bi khairin ma anta … – Al’ummata ba za ta gushe ba tana cikin alkairi matukar tana yin buda-baki sannan kuma ta jinkirta sahur”. Shi buda-baki ana son gaggautawa, sahur kuma ana son jinkirtawa zuwa karshen dare.

An karba daga Abdullahi bin Maz’unu yana cewa Sahabban Manzon Allah (SAW) sun kasance mafi gaggawar mutane buda-baki sannan mafi jinkirin mutane sahur. Baihaki ne ya ruwaito hadisin da sanadinsa ingantacce.

Abu Dawud ya ce, Abu Abdullahi ya ce “Idan Mutum ya yi kokonto cikin alfijir to ya yi ta cin abincinsa har sai ya sakankance alfijir ya futo.” Wannan ita ce nasabar Abdullahi bin Abbas da Adda’u da Auza’i da Ahmadu bin Hambali.

An karba daga Anas Allah ya kara yarda da shi ya ce “Manzon SAW ya kasance yana buda-baki da danyen dabino, in ba a samu danye ba sai ya yi da busassshe idan ba a samu ba sai ya sha ruwa kadan”. Abi Dawud da Tirmizi suka ruwaito Hadisin. Addinin Musulunci balaraben addini ne, dabino yana daga cikin alamun addinin musulunci don haka ya dace gwamnati ta kula da sana’ar dabino musammam lokacin azumin watan Ramadan. Sabida wannan dabinon da muke buda baki da shi, ba musan shekararsa nawa da yanko shi kasa ba.

Amma akwai wata hikima da ake yi wajen maida busassshen dabino zuwa danyen dabino. Da safe, sai mutum ya dibo iya wanda zai yi buda baki da shi, ya wanke dabinon, sai ya nemo ruwan zafi, ya jika a ciki sai ya kulle robar da ya jika dabinon zuwa lokacin buda-bakin.

 

Kiyaye harshe daga alfasha

An karba daga Abi Huraira Allah ya kara yarda da shi, shi kuma ya karba daga Manzon Allah (SAW) ya ce “Azumi ba wai barin ci da sha ne kawai azumi ba, azumi barin maganar batsa da maganar da ba ta dace ba, idan wani ya zage ka ko ya dame ka, to ka ce masa ni ina azumi”, Hakim ya ce ingataccen hadisi ne.

“Manzon Allah (SAW) ya ce duk wanda bai bar gulma da kagen karya da kitsa sharri ba a azumi, Allah ba shi da wata bukata da azuminsa.”

Ya zo daga Annabi (SAW) yana cewa “da yawa wasu ba su da Ladan azumi sai dai wahalar kishirwa da shan yunwa kawai, da yawa mutum ke sallar dare amma ba su da ladan sallar sai dai wahalar tsayuwa kawai.” Hadisin Ingatacce ne abisa sharadin Bukhari.

 

Yin aswaki da azumi abu ne mai kyau

Asiwaki da kyauta da yawaita karatun Alkur’ani da yawaita ibadu a cikin watan Ramadan duk Allah yana son hakan musamman a goman karshe ta watan.

Ya zo a cikin ingatattun hadisai daga Amiru yana cewa “da yawa na ga Annabi (SAW) ba daya ba biyu ba kai ba za su kidayu ba yana yin asiwaki kuma yana cikin azumi.”

Sayyada A’isha uwar Muminai ita kuma ta saukaka ta ce mutum zai iya sa abun kamshin baki a bakinsa, don bakin ya zama ba ya wari ya yi kamshi, sabida su Larabawa al’adarsu suna sumba, sharadi dai kar ya shiga makogoro. Wannan ijtihadi ne na Sayyada A’isha. Mace mai girki ta iya dandanar gishiri sai ta tofar ko mai sana’a irin wacce sai an dandana ake gane ingancin sana’ar, za su iya dandanawa sai su zubar. Haka mai alwala, in ya tofar da ruwan bakinsa sau uku, abin da ya biyo baya ba ruwa ba ne, miyau ne.

Bukhari ya ruwaito daga Abdullahi bin Abbas cewa Manzon Allah (SAW) shi ne mafi kyautar mutane amma babban lokacin kyautar Manzon Allah (SAW) ita ce Ramadan, lokacin da Mala’ika Jibrilu ke zuwa su yi musaffar Alkur’ani.

Duk abin da Mala’ikah Jibrilu ya zo wa Annabi da shi a wannan shekara, to sai sun yi musaffar wannan karatun a watan Ramadan. Sabida haka ne Annabi (SAW) yake ninka kyautarsa a watan Ramadan.

An ruwaito daga Sayyada A’isha ta ce Annabi (SAW) idan goman karshen watan Ramadan ta shigo yana raya daren duka.

Mai azumi zai iya shiga Shawa ya yi wanka, zai iya shiga kogi matukar ruwa ba zai shiga cikinsa ba, mai azumi zai iya zuba ruwa a kansa don ya ji sauki, kuma zai iya kuskure bakinsa. Ba laifi don an yi kiran sallar fitowar alfijir, mutum ya yi wankan Janaba. Wanda ya yi mafarkin saduwar aure da rana a watan azumi bai bata masa azumi ba,. Wanda ruwa ya kubuce masa lokacin alwala, azuminsa bai lalace ba, amma zai rama daya bayan Ramadan. Kurar kan hanya ba za ta bata wa mutum azumi ba, duk abin kasuwancin da sai an dandana ake gane ingancinshi, dandanawar ba za ta karya azumin ba.

Abin da ke karya azumi sun hada da: janyo amai da gangan, zuwan haila, zuwan haihuwa, janyo maniyyi da gangan, ci ko sha daga fitowar alfijir zuwa faduwar rana, saduwa da iyali daga futowar alfijir zuwa faduwar Rana.

Mutum wanda zai ba da zakkar buda-kai zai iya yin ta yanzun (farkon azumi) ya bai wa talakan da bai da dama don ya samu abun buda-baki da shan ruwa.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Annabi SAW Ya Zarce Duk Sauran Annabawa Yawan Mu’uzijoji
Dausayin Musulunci

Annabi SAW Ya Zarce Duk Sauran Annabawa Yawan Mu’uzijoji

December 12, 2025
Allah Ya Bai Wa Annabi (SAW) Mu’ujizozi Fiye Da 2,000 A Alƙur’ani   
Dausayin Musulunci

Allah Ya Bai Wa Annabi (SAW) Mu’ujizozi Fiye Da 2,000 A Alƙur’ani  

December 5, 2025
Allah Ya Bai Wa Annabi (SAW) Mu’ujizozi Fiye Da 2,000 A Alƙur’ani
Dausayin Musulunci

Allah Ya Bai Wa Annabi (SAW) Mu’ujizozi Fiye Da 2,000 A Alƙur’ani

November 28, 2025
Next Post
Goron Sallah

GORON JUMA'A

LABARAI MASU NASABA

Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

December 21, 2025
Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

December 21, 2025
Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

December 21, 2025
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

An Cafke Wani Mutum Da Ya Lakada Wa Dansa Duka Har Lahira A Edo

December 21, 2025
Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

December 21, 2025
Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

December 21, 2025
Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

December 20, 2025
Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin

Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin

December 20, 2025
Matasa Miliyan 80 Ne Ba Su Da Aikin Yi A Nijeriya

Matasa Miliyan 80 Ne Ba Su Da Aikin Yi A Nijeriya

December 20, 2025
An Nuna Jigo Da Tambarin Shagalin Murnar Bikin Bazara Na Shekarar 2026 A Moscow

An Nuna Jigo Da Tambarin Shagalin Murnar Bikin Bazara Na Shekarar 2026 A Moscow

December 20, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.