Kwanan nan ne wakilin babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG, ya zanta da Konstantin Novoselov, mai lambar karramawa ta Nobel a fannin ilimin fiziks. Novoselov wanda ya samu lambar karramawar lokacin da yake da shekaru 36 a duniya, ya ce, kaifin basirar dan Adam a ko yaushe, shi ne tushen gano kimiyya da tunanin kirkire-kirkire.
Da yake bayyana yadda idanuwansa suka shaida ci gaban kimiyya da fasaha da kasar Sin ta samu karkashin shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar, Konstantin Novoselov ya bayyana farin-cikin ganin an samu nasarorin fasaha na zahiri, sakamakon aiwatar da manufofin shirin.
Yayin da hadin gwiwar nazarin kimiyya tsakanin kasa da kasa ke fuskantar kalubale daga siyasar duniya a halin yanzu, Konstantin Novoselov, ya ce ba za a iya raba mu’amala da hadin gwiwar kasa da kasa da ci gaban kimiyya ba, inda ya yi fatan ganin ci gaba da karfafar irin wannan hadin gwiwa a nan gaba. (Murtala Zhang)














