A ranar 17 ga watan Satumba ne, aka jefa kuri’a a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, dangane da kudurin tsawaita wa’adin rukunin kwararru mai kula da takunkuman da aka kakaba wa Iran da Amurka ta gabatar, inda Rasha da Sin suka jefa kuri’ar ‘na ki’, al’amarin da ya sa ba a amince da daftarin kudurin ba.
A ranar 1 ga watan Oktoba kuma, babban taron MDD karo na 81 ya kira wani cikakken zama dangane da yadda kasashe masu kujerun dindindin suka yi amfani da hakkinsu na jefa kuri’ar na ki, inda zaunannen wakilin kasar Sin da ke MDD, Sun Lei ya bayyana cewa, ya zama dole a ki yarda da duk wani yunkuri na tsananta rikici da kawo illa ga shawarwari. Sai dai kuma, dole ne a mayar da hankali kan duk wata damar da ka iya sassauta halin da ake ciki gami da taimaka wa kokarin diflomasiyya.
Sun Lei, ya kara da cewa, mawuyacin halin da batun nukiliyar Iran ya shiga, ya samo asali ne daga janyewar Amurka daga yarjejeniya ta dukkanin fannoni, gami da yadda ta yi bakin kokarin matsa wa Iran lamba, tare kuma da daukar matakan soja har sau biyu yayin da ake tsaka da shawarwari tsakaninta da Iran. A ganin kasar Sin, jirkita gaskiyar tarihin batun nukiliyar Iran, gami da kara kokarin farfado da sanya wa Iran takunkumi da kuma gabatar da daftarin kuduri da ka iya haifar da rikici, tabbas zai lahanta hadin gwiwa da kwarjinin kwamitin sulhu na MDD, da kuma taka birki ga kokarin diflomasiyya. (Murtala Zhang)














