Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya isa Washington DC a jirgin sama na musamman ran 23 ga watan Satumba da yammacin agogon kasar, domin ziyarar aiki a kasar bisa gayyatar shugaban Amurka Donald Trump.
Lokacin da Xi da uwargidansa Peng Liyuan suka isa sansanin sojin sama na Andrews a Washington DC, Trump da uwargidansa Melania Trump sun yi musu kyakkyawar tarba. Trump ya ce, yana farin cikin karbar shugaba Xi da uwargida Peng Liyuan a Washington DC, kuma wannan ziyara ta jawo hankalin kasa da kasa matuka. Yana fatan yin musayar ra’ayi mai zurfi da shugaba Xi, domin ingiza ci gaban dangantakar kasashen biyu.
Xi a nasa bangare, ya yi jawabi a rubuce, inda a madadin al’ummar Sinawa, ya mika gaisuwa da fatan alheri ga al’ummar Amurkawa. Xi ya nuna cewa, ya kamata Sin da Amurka su bi hanya iri daya da ingiza tabbatar da dangantaka mai dorewa da za ta fi mayar da hankali kan hadin gwiwa da yin takara yadda ya kamata, da daidaita bambancin ra’ayi, da shimfida zaman lafiya, kuma su bi hanyar da ta dace ta yadda manyan kasashe biyu za su yi mu’amala da juna a sabon zamani.(Amina Xu)














