ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Monday, October 26, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Ƴan Bindiga Suka Yanke Min Yatsu Biyu — Masunci A Kaduna

by Abubakar Sulaiman
6 days ago

Wani masunci kuma mahaifin ƴaƴa huɗu mai suna Ibrahim Abubakar, ya bayyana yadda wasu ƴan bindiga suka datse masa yatsu biyu a yayin da yake ƙoƙarin tserewa don tsirar da ransa a lokacin wani hari a garin Maraban Jos da ke Jihar Kaduna.

Abubakar ya bayyana halin da yake ciki a ranar Talata, 20 ga watan Oktoba, 2026, inda ya bayyana cewa maharan sun kai harin ne tsakanin ƙarfe 1:00 zuwa 2:00 na daren ranar 9 ga watan Agusta, 2026.

Da yake bayyana yadda lamarin ya auku, masuncin ya ce ƴan bindigar sun kutsa kai cikin garin ne domin yin fashi da kwashe kayan al’umma.

ADVERTISEMENT

Ya ce ya farka daga barci cikin firgici ya fara ranta a na kare, amma maharan suka tare shi tare da datse masa yatsu biyu a hannunsa kafin ya samu nasarar kuɓucewa, lamarin da ya bar shi cikin mawuyacin hali da zubar da jini.

Wannan mummunan rauni ya jefa rayuwar Abubakar cikin ƙalubale, musamman yadda ya gaza ci gaba da aikin kamun kifi da ya dogara da shi domin ciyar da kansa da iyalinsa. Ya bayyana cewa yana cikin matsanancin damuwa da ciwo, tare da fuskantar cikas wajen ɗaukar dawainiyar ƴaƴansa huɗu tun bayan aukuwar wannan harin.

LABARAI MASU NASABA

EFCC Ta Buɗe Shafin Ɗaukar Ma’aikata Na 2026, Duba Sharuɗɗan Neman Aikin

Wa’adin INEC Ya Ƙare: Ina Makomar Takarar Aminu Gwarzo A Kano Da Pantami A Gombe?

Abubakar ya yi kira ga gwamnati, ƙungiyoyin agaji, da sauran al’umma masu hannu da shuni da su tallafa masa da kuɗin magani domin samun cikakkiyar kulawar asibiti.

Wannan lamari ya sake fito da irin halin ƙuncin da hare-haren ƴan bindiga ke jefa talakawan karkara a Jihar Kaduna, waɗanda ke ci gaba da fuskantar barazana a rayuwarsu da harkokin neman abinci.

Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Wata Mata Ta Caka Wa Mijinta Wuƙa Kan Rigimar Wayar Salula A Bauchi
  • Abubakar Sulaiman
    Nan Gaba Kaɗan Zan Bayyana Waɗanda Ke Daƙile Takarata – Pantami
  • Abubakar Sulaiman
    Ƴan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Manoma 2 A Wani Sabon Hari A Kaduna
  • Abubakar Sulaiman
    NCDC Za Ta Fara Biyan Mutanen Da Aka Killace ₦100,000 Saboda Ebola

MASU ALAKA

EFCC Ta Buɗe Shafin Ɗaukar Ma’aikata Na 2026, Duba Sharuɗɗan Neman Aikin
Manyan Labarai

EFCC Ta Buɗe Shafin Ɗaukar Ma’aikata Na 2026, Duba Sharuɗɗan Neman Aikin

October 25, 2026
Wa’adin INEC Ya Ƙare: Ina Makomar Takarar Aminu Gwarzo A Kano Da Pantami A Gombe?
Siyasa

Wa’adin INEC Ya Ƙare: Ina Makomar Takarar Aminu Gwarzo A Kano Da Pantami A Gombe?

October 25, 2026
Kwamitin Zartarwa Na ADC Na Ƙasa Ya Yi Watsi Da Bangaran David Mark Da Bala Gombe, Ya Naɗa Shugabancin Riƙo
Siyasa

ADC Ta Yi Wa APC Ba’a Kan Zargin Hayar Taron Jama’a Da Rashin Cika Kujeru A Taron Kaduna

October 25, 2026
Next Post
Ƴan Bindiga Sun Kashe Jami’in Tsaron Daji A Nasarawa

Ƴan Bindiga Sun Kashe Jami’in Tsaron Daji A Nasarawa

LABARAI MASU NASABA

Wata Mata Ta Caka Wa Mijinta Wuƙa Kan Rigimar Wayar Salula A Bauchi

Wata Mata Ta Caka Wa Mijinta Wuƙa Kan Rigimar Wayar Salula A Bauchi

October 25, 2026
An Yi Taron Karawa Juna Sani Na Murnar Cika Shekaru 81 Da Maido Da Taiwan Kasar Sin A Birnin Fuzhou

An Yi Taron Karawa Juna Sani Na Murnar Cika Shekaru 81 Da Maido Da Taiwan Kasar Sin A Birnin Fuzhou

October 25, 2026
Nan Gaba Kaɗan Zan Bayyana Waɗanda Ke Daƙile Takarata – Pantami

Nan Gaba Kaɗan Zan Bayyana Waɗanda Ke Daƙile Takarata – Pantami

October 25, 2026
Xi Da Sarki Philippe Na Belgium Sun Taya Juna Murnar Cika Shekaru 55 Da Kulla Alakar Kasashensu

Xi Da Sarki Philippe Na Belgium Sun Taya Juna Murnar Cika Shekaru 55 Da Kulla Alakar Kasashensu

October 25, 2026
Mai Taimaka Wa Babban Sakataren MDD Ya Yaba wa Kasar Sin Bisa Hangen Nesanta

Mai Taimaka Wa Babban Sakataren MDD Ya Yaba wa Kasar Sin Bisa Hangen Nesanta

October 25, 2026
Ƴan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Manoma  2 A Wani Sabon Hari A Kaduna

Ƴan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Manoma 2 A Wani Sabon Hari A Kaduna

October 25, 2026
NCDC Za Ta Fara Biyan Mutanen Da Aka Killace ₦100,000 Saboda Ebola

NCDC Za Ta Fara Biyan Mutanen Da Aka Killace ₦100,000 Saboda Ebola

October 25, 2026
Sin Ta Harba Sabon Rukunin Taurarin Dan Adam Na Intanet

Sin Ta Harba Sabon Rukunin Taurarin Dan Adam Na Intanet

October 25, 2026
Farashin Tumatir Ya Tsiri, Na Barkono Ya Sauka A Legas

Farashin Tumatir Ya Tsiri, Na Barkono Ya Sauka A Legas

October 25, 2026
Jami’in WHO: Kasar Sin Na Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Habaka Ci Gaban Magungunan Gargajiya A Duniya

Jami’in WHO: Kasar Sin Na Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Habaka Ci Gaban Magungunan Gargajiya A Duniya

October 25, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.