Xi Jinping, babban sakataren kwamitin tsakiya na jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin (CPC), ya yi kira da a yi kokarin amfani da fa’idodin auna abubuwa da kasar ke da su wajen samun ci gaba tare da kiyaye kwanciyar hankali, da karfafa ci gaba da samun sabbin nasarori a fannin habaka masana’antu na gaba.
Xi ya yi wannan tsokaci ne yayin da yake jagorantar zaman nazari na ofishin siyasa na babban kwamitin tsakiya na jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin a ranar 30 ga watan Janairu.
Ya yi nuni da cewa kafawa da habaka masana’antu na gaba na da matukar muhimmanci ga samun nasara a fannin gasar kimiyya, fasaha da masana’antu, da kuma daukar matakai a fannin samar da ci gaba. Haka kuma yana da matukar muhimmanci ga bunkasa sabbin ginshikai masu inganci, da gina tsarin masana’antu na zamani, da inganta rayuwar jama’a, da karfafa ci gaban bil’adama da ya kunshi komai da komai da kuma kyautata ci gaban zamantakewa gaba daya. (Abdulrazaq Yahuza Jere)















Discussion about this post