Shugaban kasar Sin Xi Jinping, da wasu jami’an JKS, da shugabannin gwamnati, za su aza kwandunan furannin karrama ‘yan mazan jiya, da suka rasa rayukansu wajen bautawa kasa albarkacin ranar jaruman kasar, a filin taruwar jama’a na Tian’anmen dake tsakiyar birnin Beijing da safiyar ranar Laraba.
Shugabannin za su hadu da wakilai daga sassan rayuwa daban daban yayin bikin aza furannin, wanda za a watsa kai tsaye ta kafar CMG ta kasar Sin.
A shekarar 2014, babbar majalisar dokokin kasar Sin ta yanke shawarar kafa ranar jaruman kasa, wadda ake bikinta a duk ranar 30 ga watan Satumba, kwana guda kafin bikin ranar kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin, ana kuma amfani da ranar wajen tunawa da mutanen da suka sadaukar da rayukansu domin samar da ‘yanci da ci gaban kasar Sin. (Saminu Alhassan)














