Rundunar ’yansandan jihar Kaduna ta hana zirga-zirgar manyan motoci a cikin jihar daga tsakar dare zuwa ƙarfe 8 na daren ranar Asabar, gabanin ziyarar Shugaba Bola Tinubu.
Ana sa ran Tinubu zai halarci ƙaddamar da gangamin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC a Kaduna.
Kwamishinan ’yansandan jihar, Muhammad Rabiu, ya ce an ɗauki matakin ne domin rage cunkoson ababen hawa da kuma sauƙaƙa zirga-zirga yayin ziyarar.
Ya bayyana cewa dokar ta shafi tireloli, tankokin dakon mai, manyan motocin dakon kaya da sauran manyan motoci.
Rundunar ’yansanda da sauran jami’an tsaro sun shirya tura jami’ai domin tabbatar da tsaron shugaban ƙasa, manyan baƙi da sauran al’umma.
’Yansandan sun kuma shawarci mazauna jihar da su guji zuwa wajen taron gangamin idan ba su da wani muhimmin aiki a wajen.
Sun yi gargaɗi kan duk wani nau’in tashin hankali na siyasa, daba, tsoratarwa da kuma ɗaukar makamai masu haɗari.
An kuma shawarci direbobin manyan motoci da su bi wasu hanyoyi na daban yayin da dokar ke aiki.
Kwamishinan ya buƙaci mazauna jihar, magoya bayan jam’iyyun siyasa da kafafen yaɗa labarai da su ba jami’an tsaro haɗin kai domin tabbatar da gudanar da taron cikin lumana.












