Hukumar kare fararen hula ta Saudiyya ta fitar da gargaɗi da safiyar Juma’a ga mazauna babban birnin ƙasar, Riyadh, inda ta buƙaci su koma wurare masu aminci domin kare kansu daga hare-haren da ake sa ran za su iya faruwa nan ba da jimawa ba.
Sai dai bayan ƴan mintoci kaɗan hukumar ta fitar da wannan gargaɗi. A lokaci guda kuma, ta wallafa wani saƙo a shafinta na sada zumunta tana mai cewa haramun ne ɗaukar bidiyo ko yaɗa hotuna da bidiyon tsarin kariya daga hare-haren makamai masu linzami da jiragen yaƙi marasa matuƙa.
BBC Hausa ta ruwaito cewa, a halin da ake ciki, wasu kafafen yaɗa labarai sun rawaito cewa an ji ƙarar fashewa a birnin Riyadh, amma har yanzu babu wani cikakken bayani da hukumomi ko wasu majiyoyi masu zaman kansu suka tabbatar game da lamarin.













