Kamfanin Simintin Dangote, masana’antar Gboko, ya bayar da tallafin karatu na miliyoyin Naira ga daliban manyan makarantu da na sakandare daga al’ummomin da ke karbar bakuncin masana’antar guda shida a Jihar Benue.
Kamfanin ya kuma gabatar da kayan fara sana’a, kayan aiki da takardun shaidar kammala horo ga wadanda suka kammala shirin karfafa wa matasa, domin ba su damar kafa sana’o’insu, amfani da kwarewar da suka samu yayin horo da kuma dogaro da kansu ta fuskar kudi.
Ministan Ma’adanan Karkashin Kasa, Dr. Henry Dele Alake, ya yaba wa Kamfanin na Simintin Dangote bisa ayyukan ci gaban al’umma da yake gudanarwa, inda ya yi kira ga sauran kamfanoni masu zaman kansu da su rungumi irin wadannan shirye-shirye domin bunkasa tattalin arziki da zamantakewa a al’ummomin da suke karbar bakuncinsu.
Dr. Alake, wanda Injiniya Achi Gregory, Jami’in Ma’adanai na Tarayya na Ma’aikatar Ma’adanan Karkashin Kasa a Jihar Benue, ya wakilta, ya bukaci kamfanin da ya ci gaba da jajircewa wajen aiwatar da shirye-shiryen ci gaban al’umma da aka amince da su tare da al’ummomin da ke karbar bakuncinsa.
Da yake jawabi a wajen bikin mika kayan, Shugaban Rukunin Ayyukan Zamantakewa na Kamfanin Simintin Dangote, Mista Wakeel Olayiwola, ya ce aiwatar da Yarjejeniyar Ci Gaban Al’umma na nuna jajircewar Kamfanin Simintin Dangote wajen samar wa matasa kwarewar aiki da kayayyakin da za su taimaka musu wajen bunkasa sana’o’i, samar da guraben ayyukan yi da inganta rayuwar al’ummomin da ke karbar bakuncin masana’antar.
Mista Olayiwola, wanda Shugaban Ayyukan Zamantakewa na masana’antar Dangote da ke Gboko, Dr. Johnson Kor, ya wakilta, ya ce shirye-shiryen bayar da tallafin karatu da karfafa matasa sun zo ne bayan wasu shirye-shirye da dama da kamfanin ya aiwatar kwanan nan, wadanda suka hada da shirye-shiryen karfafa manoma da mata.
Muƙaddashin Daraktan Kamfanin Simintin Dangote na Gboko, Injiniya Arbind Singh, ya ce: “Wannan shirin bayar da tallafin karatu na shekara-shekara ga dalibai marasa galihu daga al’ummomin da ke karbar bakuncin masana’antar, yana nuna jajircewar kamfaninmu wajen sauke nauyin da ke kansa na zamantakewa (CSR).”
Injiniya Singh, wanda Babban Manajan Kamfanin na Samar da Kayayyaki, Injiniya Tabershima Soom, ya wakilta, ya ce: “Masana’antar Gboko ta riga ta kaddamar da shirin karfafa wa mata 150 da kuma shirin karfafa wa manoma 50, inda aka bai wa mata kudi domin tallafa wa sana’o’insu, yayin da aka tallafa wa manoma da kayan aikin noma.” Al’ummomin da suka amfana da wadannan shirye-shirye su ne: Tse-Kucha, Quarry, Amua, Mbazembe, Mbatur da Pass Brothers.
Da yake magana a madadin Babban Lauyan Gwamnatin Jihar Benue, Shugaban Kwamitin Kula da Albarkatun Ma’adanai da Muhalli (MIREMCO), Barr. Dooshima Orosaga, ya yaba wa Kamfanin Simintin Dangote bisa bin ka’idojin Yarjejeniyar Ci Gaban Al’umma (CDA), tare da kira ga wadanda suka amfana da al’ummomin da ke karbar bakuncin kamfanin da su yi amfani da damar da shirye-shiryen kamfanin suka samar domin samun ci gaba.
Shugaban Karamar Hukumar Gboko, Hon. Yina Elias, ya ce gwamnati za ta ci gaba da bayar da goyon bayan da ake bukata domin kamfanin ya samu nasara, yana mai kara da cewa Kamfanin Simintin Dangote kamfani ne abin koyi wajen gudanar da shirye-shiryen daukar nauyin zamantakewa (CSR).
A nasa jawabin, Hakimin Ukpekpe, Cif Tsegba Igbarumun, ya yaba wa masana’antar Dangote Cement ta Gboko bisa gudummawar da take bayarwa ga al’umma, tare da tabbatar wa kamfanin cewa al’ummar za ta ci gaba da ba shi goyon baya.
Ya ce al’ummar suna daraja kyakkyawar dangantakar da ke tsakaninsu da kamfanin, wadda ke amfanar da bangarorin biyu, kuma za su ci gaba da kasancewa jakadun kamfanin.
Daya daga cikin wadanda suka amfana da Shirin Karfafa Wa Matasa, Mista Ignatius Aondohemba, ya nuna godiyarsa ga Kamfanin Simintin Dangote bisa tallafin da ya samu, tare da alkawarin yin amfani da kwarewa da kayan aikin da aka ba shi yadda ya kamata, da kuma kafa sana’ar da za ta ba shi damar zama mai daukar ma’aikata.












