Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun, ya ce kamata ya yi sassan kasa da kasa su yi kira ga kasar Japan, da ta martaba yarjejeniyoyin nan uku na hana mallakar nukiliya, kana ta cika alkawuran da ta dauka dangane da hana bazuwar makaman nukiliya, ta kuma yi watsi da yunkurinta na farfado da karfin soji da mallakar nukiliya.
Guo Jiakun, ya bayyana hakan ne a Larabar nan, yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa, yayin da yake martani bayan da aka jiyo shugaban sashen tsaron kasar Japan na yanzu, na cewa bai kamata Japan ya ji kunyar tattauna batun mallakar makaman nukiliya, da jirgin ruwa mai nutso a teku dake aiki da makamashin nukiliya ba.
Jami’in ya kara da cewa, Sin na goyon bayan warware rashin jituwa ta hanyar siyasa da diflomasiyya, tana kuma fatan Iran da Amurka za su rungumi zabin zaman lafiya, su komawa yarjejeniyar fahimtar juna ta Islamabad, kana su gaggauta komawa tattaunawa da shawarwari. (Saminu Alhassan)














