A gun taron tattaunawa kan zuba jari da kasuwanci na sassan kasa da kasa na kasar Sin, wato CIFIT karo na 26 da aka gudanar daga ranar 8 zuwa 11 ga wannan wata, Mohammed Y. Al Qahtani, shugaban sashen kananan ayyuka na kamfanin Aramco na kasar Saudiyya ya bayyana cewa, yawan jarin da kamfanin ya zuba a kasar Sin ya zarce dalar Amurka biliyan 33, yana cewa kasar Sin ba muhimmiyar kasuwa ba ce kadai, ta kasance muhimmiyar abokiyar hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare na dogon lokaci.
A gun taron, shugabannin kamfanonin kasa da kasa sun bayyana cewa, ya kamata a rike damar kasar Sin samfurin 2.0, da ayyana ziyararsu a kamfanonin kasar Sin, a matsayin muhimmiyar dama ta kara fahimtar yanayin sassan kasar Sin da yadda za a rike damarmakin da kasar Sin take da su.
A matsayin babban taro daya tilo dake shafar zuba jari a kasar Sin, taron ya samu sabon ci gaba a wannan karo, inda aka gudanar da shi a shekarar farko na aiwatar da shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 15 na kasar Sin, kuma adadin kasashe da kungiyoyi mahalartar ya kai matsayin koli a tarihi, fadin murabba’in taron shi ma, ya kai matsayin koli, inda kasashe biyu wato Finland da Saudiyya suka kasance kasashe manyan baki a gun taron a karo na farko.
Haka kuma an kafa shagunan musamman na shaida sabon karfin samar da hajoji da hidimomi masu karko da na hadin gwiwar kamfanonin kasa da kasa kan fasahohin zamani da sauransu wadanda suka shaida mutum-mutumin inji da na’urorin fasahar zamani da sauransu.
A yayin da duniya take cikin lokacin fuskantar sabon sauyin yanayi, an yi musayar ra’ayoyi da shawarwari da dama a gun taron CIFIT, wanda ya shaida cewa, bude kofa da hadin gwiwa, aiki ne mai dacewa a halin yanzu, kana samun moriyar juna ya biya bukatun jama’a baki daya. (Zainab Zhang)














