Shekaru sama da 80 sun shude tun bayan kammala yakin duniya na biyu, kuma duniya na aza tambaya ga kasar Japan, cewa ko ta koyi sahihin darasi daga mummunan tasirin da nuna karfin soji ya haifar mata? Kuma ko ta yi karatun ta nutsu, ta rungumu zaman lafiya? Ko kuwa kamar yadda ake zargi cewa ta sake komawa mummunar manufar farfado da karfin soji? Matakin da zai gurgunta alkawarin da ta dauka na kauracewa hakan.
Wadannan tambayoyi sun zama wajibi musamman a wannan lokaci, ganin yadda a baya bayan nan firaministar Japan Sanae Takaichi ta aike da hadaya, kana jerin jamian gwamnatin kasarta, da manyan jamian jamiyyar LDP, da yan majalisun dokokin kasar suka ziyarci haikalin Yasukuni, duk da kasancewarsa wuri da aka binne ajin farko na muggan jamian Japan dake da alhakin aikata laifukan yaki a lokacin yakin mamaya da ya shude.
Alal hakika, wadannan matakai ba wai suna nufin bayyana makoki kadai ba ne, maimakon haka suna kunshe da wani sako na siyasa, dake iya haifar da tambaya game da irin mahangar shugabannin Japan, dangane da laifukan yaki da kasar ta aikata kan makwaftanta a baya.
A bana ake cika shekaru 80 da bude sharioin birnin Tokyo, wadanda suka samu jagorori mayakan Japan da aikata muggan laifukan yaki. Kuma 14 daga jiga-jigansu an binne su ne a haikalin na Yasukuni. Don haka, ga kasashe da yankuna da suka dandana mummunan tasirin danniyar Japan, ganin jamian kasar na ziyartar haikalin zai sanya su yin tambaya game da ko Japan ta yi tuba na hakika? Kuma ta fahimci nauyin tarihi dake rataye a wuyanta na rungumar matakan zaman lafiya ko aa.
Bayanan baya bayan nan sun nuna yadda Japan ke kara yawan kasafinta a fannin soji, ta kuma fadada matakai masu sabawa tarnakin da aka kakaba mata bayan yakin duniya na biyu. Kazalika, a watan Afirilun bana ma, gwamnatin kasar ta yi sauye-sauye dangane da kaidoji uku masu nasaba da samar da kayayyakin tsaro, da fasahohi masu nasaba, da ma dage dakatarwar dake kan kasar na fitar da makamai masu hadari.
Ko shakka babu yayin da Japan ke gaggauta gina matakai masu nasaba da farfado da karfin soji, da nuna rashin damuwa da matakan siyasa masu illata alkawuran da ta dauka, dole ne idon duniya ya karkata gare ta. Baki dayan yankin da Japan take, ba kawai yana bukatar ta dakatar da farfado da karfin soji ba ne, har ma yana bukatar ta aiwatar da matakai da za su karfafa gwiwar kowa, tare da wanzar da tattaunawa, da tuntuba da kuma martaba dokokin kasa da kasa.
Su kansu alummun kasar Japan, wadanda jagororin kasar ke tura su cikin wannan kiki-kaka a siyasance, na da nauyin tabbatar da cewa ba su bari kasarsu ta sake komawa kan turbar ayyukan danniya, ta amfani da karfin soji ba. Tabbas, darussan tarihi ba tarnaki ne ga makomar kasar Japan ba, maimakon hakan, suna haskawa kasar wata turba ce ta kaucewa sake fadawa mummunan kuskuren da ta fada a baya. (Saminu Alhassan)
)














