Mazauna unguwar Madina da ke cikin birnin Bauchi sun musanta iƙirarin Dahiru Abubakar, wanda aka fi sani da “Jejiwe Ɗan Malam”, na cewa an cire shi daga mukaminsa na limami saboda tallata Shugaba Bola Ahmed Tinubu gabanin zaɓen.
Wasu mazauna unguwar sun ce Dahiru Abubakar ba shi ne asalin limamin masallacin da ake magana a kai ba, yayin da wasu suka bayyana cewa yana jagorantar sallah ne lokaci-lokaci idan babban limamin masallacin ba ya nan, wanda kowa na iya yin hakan.
Sai dai Dahiru Abubakar ya dage cewa an cire shi daga masallacin da ya kasance yana jagorantar sallah tare da yin wa’azi lokaci-lokaci, inda ya yi zargin cewa goyon bayansa da kuma kamfen ɗin da yake yi wa Tinubu sun taimaka wajen ɗaukar matakin cire shi.
Da yake zantawa da wakilinmu, wani mazaunin unguwar mai suna Ibrahim Muhammad, wanda ya ce yana da masaniya kan lamarin, ya bayyana Abubakar a matsayin mutum mai yawan jawo ce-ce-ku-ce, wanda a cewarsa yake hulɗa da ’yan siyasa daga jam’iyyu daban-daban.
Muhammad ya yi zargin cewa a baya Abubakar ya sha sukar Tinubu da jam’iyyar APC kan matsin tattalin arzikin da ake fuskanta a ƙasar, kafin daga bisani ya bayyana goyon bayansa ga shugaban ƙasar.
“Duk wanda ya san ‘Jejiwe Ɗan Malam’ ya san shi a matsayin mai barkwanci da kuma mutum mai yawan jawo ce-ce-ku-ce. Yana aiki da kusan kowace jam’iyyar siyasa,” in ji shi.
Ya ƙara da zargin cewa watannin baya, Abubakar ya ɗora wa Tinubu alhakin wahalhalun da ake fuskanta a ƙasar tare da sukar jam’iyyar APC.
Muhammad ya yi iƙirarin cewa ra’ayoyin siyasar Abubakar suna canzawa gwargwadon yanayin da ake ciki, inda ya bayyana cewa yana ganin wannan batu na baya-bayan nan wata hanya ce ta neman ɗaukar hankalin jama’a.
Ya shawarci ’yan jarida da sauran jama’a da su riƙa taka-tsantsan wajen yaɗa bayanai, musamman a daidai lokacin da harkokin siyasa ke ƙara ƙamari gabanin zaɓen shekarar 2027.
“A wannan lokacin siyasa, kowa zai nemi hanyar jawo hankalin jama’a. Saboda haka, yana da muhimmanci ’yan jarida su tabbatar da sahihancin bayanai kafin su yaɗa su,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa bai kamata a riƙa jawo addini cikin saɓanin siyasa ko amfani da shi a matsayin hanyar neman wata moriyar kai ba.
Wani makusancin Danmalam, wanda shi ma mazaunin unguwar ne, ya bayyana cewar Dahiru Abubakar ba shi ne asalin limamin masallacin ba.
A cewar mutumin, Abubakar yana jagorantar sallah ne kawai idan asalin limamin masallacin ba ya nan.
“Ba shi ne asalin limamin masallacin ba. Yana jagorantar sallah ne kawai idan ainihin limamin ba ya nan. Wannan shi ne kawai,” In ji shi.
Haka kuma, Adamu Garba, wani mazaunin unguwar Madina Quarters, ya musanta iƙirarin cewa Abubakar ne limamin masallacin.
Garba, wanda ya ce yana zaune a layin da ke kusa da makarantar Barden Gabas a unguwar, inda ake zargin masallacin yake, ya bayyana cewa su ma mazauna unguwar labarin ne kawai suke ji yana yawo a tsakanin jama’a.
Sai dai Imam Dahiru Abubakar ya hakikance cewa an cire shi daga limancin masallacin da ya kasance yana jagorantar sallah da kuma yin wa’azi lokaci-lokaci.
A bayaninsa, ya fayyace cewa ƙaramin masallacin unguwa ne, ba masallacin Juma’a ba, inda ake gudanar da sallar Juma’a da jama’a da dama ke halarta, saɓanin yadda wasu suka bayyana lamarin.
“Eh, gaskiya ne an cire ni daga masallacin da na kasance ina jagorantar sallah da kuma yin wa’azi lokaci-lokaci. Hakan ya faru ne sakamakon goyon bayan da nake bai wa Bola Tinubu,” in ji shi.
Abubakar ya bayyana cewa kare Tinubu da yake yi, musamman dangane da matsalar tsaro a ƙasar, ya taimaka wajen haifar da rashin jituwa tsakaninsa da wasu mutanen da ke sallah a masallacin.
Ya ce masu adawa da shi suna ganin goyon bayan da yake bai wa shugaban ƙasar ya wuce kima.
Ya kuma bayyana rashin jituwa kan shirin sauya sunan masallacin a matsayin wani dalilin da ya taimaka wajen jawo takaddamar.
A cewarsa, ya gabatar da shawarar sauya sunan masallacin daga “Abdurrahman Bin Zuhairu” zuwa “Sheikh Imam Bola Ahmed Tinubu Mosque”, amma shawarar ba ta samu karɓuwa ba.
“Dalili na biyu da ya sa aka cire ni shi ne, na nemi a sauya sunan masallacin zuwa ‘Sheikh Imam Bola Ahmed Tinubu Mosque’. Amma ba a karɓi wannan shawara da kyau ba,” in ji shi.
Da yake mayar da martani kan zarge-zargen cewa neman kuɗi ko shahara ne ya sa yake goyon bayan Tinubu, Abubakar ya dage cewa goyon bayan nasa na gaskiya ne.
Ya tabbatar da cewa zai ci gaba da tallan Tinubu yadda ya dace.














