Akwai yiwuwar Nijeriya ta gaza samun damar fitar da Cocoa da ake nomawa a kasar zuwa kasuwannin Tarayyar Turai (EU).
Hakan ka iya faruwa ne, idan har kasar ta gaza cimma ka’idar da EUDR ta gindaya mata daga nan zuwa watan Disambar 2025.
- Wajibi Ne Sassan Kasa Da Kasa Su Raya Ruhin Jin Kan Bil’adama
- Wadanda Suka Mutu A Wani Hadarin Ginin Gada A Sin Sun Karu Zuwa 12
Nijeriya dai, ta kasance ta hudu a duniya wajen nomansa; kana kuma, wadda take kan gaba wajen fitar da shi zuwa kasuwar duniya.
Akalla duk shekara, kananan manoma a kasar sun doshi 300,000 tare da noma tan 320,000, inda kuma fannin ke samar da riba; wadda ta kai kimanin dala miliyan 700.
Idan har Nijeriya ta gaza cimma wannan ka’ida ta EUDR, hakan zai iya jawo wa fannin gazawar fitar da shi zuwa Tarayyar Turai (EU).
An dai tsara ka’idar ta EUDR ne, domin a yi yaki da illolin muhalli da kuma sare itatuwa.
Yunkurin na daya daga cikin babban aikin yarjejeniyar EU, wadda kuma ta yi daidai da ka’idar ta Tarayyar Turan, musamman domin samar da dabarun bai wa Dazuka kariyar da ta kamata a daukacin fadin duniya baki-daya.
Kazalika, burin da EU ke son cimma shi ne, magance matsalar da Dazuka ke fuskanta tare kuma da tabbatar da ana bin diddigi wajen noman na Cocoa.
Majalisar Tarayyar Turai ta bayyana cewa, ta amince da ka’idar ta EUDR a 2022, wadda kuma ta fara aiki a ranar 29 ga watan Yunin 2023.
Sai dai, ka’idar ta fara aiki ne a ranar 30 ga watan Disambar 2024, wadda kuma cibiyoyin na EU suka daga wa’adin fara aikin ka’idar zuwa ranar 30 ga watan Disambar 2025.
Har ila yau, ka’idar ta bukaci daukacin Cocoa da ake nomawa da kuma jerin sauran amfanin gona, su zamo suna samun kariya tare kuma da tabbatar da an noma su bisa ka’ida.
Su ma kananan sana’oin hannu da matsakaitan sana’oi, akwai wa’adin da aka gindaya musu na su tabbatar da sun kai kayansu, wadanda aka taskance musu zuwa watan Yunin 2026, musamman domin su tabbaar da sun samar da ingantattun kaya.
Duba da cewa, kwana hudu ne kacal suka rage, gwamnatin tarayya ta umarci hukumominta da su tabbatar da sun tsara komai bisa ka’ida, domin kada a ki amincewa da Cocoa da za a fitar da shi zuwa kasuwannin Tarayyar Turan, musamman saboda yadda wasu manoma ke zuba masa sinadaran da ke wuci kima.
Bugu da kari, a ranar Litinin da ta gabata, gwamnatin ta yunkuro wajen karfafa matakan da suka dace na masana’ar Cocoa, domin dakile saba ka’idojin yin nomansa a kasar.
An gudanar da taron tattaunawa na kara jan hankali kan karfafa ka’idar ta EUDR ne a tsakanin Nijeriya da EU, a fadar shugaban kasa da ke Abuja, musamman domin a tabbatar da Nijeriya ta cimma wa’adin ranar da aka gindaya mata.
Dakta Kingsley Uzoma, Babban Mai Taimka Wa Shugaban Kasa a bangaren noma, domin samun riba da habaka fannin noma a jawabinsa a wajen tattaunawar ya sanar da cewa, Nijeriya a shirye take wajen cika ka’idar ta EUDR.
Uzoma ya bayyana cewa, manufar tattaunawar a kan batun ka’dar ta EUDR, wadda kuma ta haramta barin fitar da Cocoa da sauran amfanin gona da suke da illa zuwa kasuwar ta EU.
Ya ci gaba da cewa, fannin na noman Cocoa wani babban ginshike ne da ke kara habaka tattalin arzikin Nijeriya.
Daga 2023 zuwa 2024, Afirka ta noma Cocoa da ya kai kimanin tan miliyan 3.151, inda Nijeriya ta noma tan 320,000 tare da kuma bukatar kara fadada nomansa zuwa tan 500,000 a 2025, ta hanyar shirye-shiryen da ta kirkiro da su.
Bisa wasu alkaluman da Hukumar Kididdga ta Kasa (NBS) ta fitar sun nuna cewa; a zango na karshe na 2024, Nijeriya ta fitar da karin Cocoa da ya kai kimanin kashi 606, wanda ya kai na kusan Naira biliyan 171 a zango na karshe na 2023 zuwa Naira biliyan 1.2.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp