Bayan kammala zaben 2023, manyan jam’iyyun siyasa a Nijeriya sun tsunduma cikin rikicin bayan zabe.
Duk da nasarar da jam’iyyar APC ta samu a zaben da aka aka kammala, jam’iyyar mai mulki ta tsunduma cikin rikicin cikin gida.
- An Shirya Bikin Yayata Shawarar Raya Kasa Da Kasa A Hedkwatar MDD
- Yadda Uwargida Za Ta Yi Kwalliyar Gida Da Sallah
Jam’iyyar ta lashe zaben shugaban kasa da na gwamna a wasu jihohi, sannan kuma ta samu kujeru masu rinjaye a majalisar dokokin kasar nan.
A daidai lokacin da ake ci gaba da farin ciki na nasarar da jam’iyyar ta samu, an samu rarrabuwar kawuna a cikinta wanda take yin barazana ga kafuwar jam’iyyar.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa mambobin kwamitin gudanarwa jam’iyyar sun tsunduma cikin rikici da ka iya wargaza jam’iyyar.
Wasu mambobin kwamitin gudanarwar jam’iyyar da wasu kungiyoyin da ke cikin jam’iyyar sun ce ba sa jin dadin salon shugabancin, Sanata Abdullahi Adamu, don haka suke ta kiraye-kirayen ya yi murabus.
A kwanakin baya an samu rahotanni a kafafen sada zumunta cewa shugaban jam’iyyar APC ya jefar da kwallon mangoro domin ya huta da kuda, amma da aka tuntubi sakataren yada labaran jam’iyyar na kasa, Felid Morka, ya ce babu kamshin gaskiya kan wannan labari.
Haka kuma, ‘yan makonni bayan zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Fabrairu, mataimakin shugaban jam’iyyar APC na kasa na yankin Arewa maso Yamma, Salihu Mohammed Lukman ya bukaci Adamu ya yi murabus.
Ya ce kamata ya yi Adamu ya yi murabus domin Kirista ya karbi mukamin shugabancin jam’iyyar, saboda a bai wa Kiristoci samun damar shiga harkokin jam’iyyar gadan-gadan.
Ya ce, “Yanzu da Tinubu ne ya lashe zaben, yana da muhimmanci a nuna cewa tikitin takarar Musulmi da Musulmi na zababben shugaban kasa da mataimakinsa Shettima dabarun zabe ne kawai.
“Tun da shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu shi ma musulmi ne, zai dace a dauki duk wani matakin da ya dace don kawo canjin shugabanci ga jam’iyyar wajen bai wa Kirista daman yin shugabancin jam’iyya.
“Daya daga cikin fa’idar hakan shi ne, ana iya ci gaba da samun shugaban kasa a yankin Arewa ta Tsakiya. Ba abu ba ne mai wahala a shawo kan Sanata Adamu ya yi murabus domin Kirista ya hau kan karagan shugabancin jam’iyyar.”
Hakazalika, wata gamayyar kungiyoyin farar hula a karkashin kungiyar masu fafutukar kare hakkin Bil’adama ta NIjeriya, ta bukaci Adamu da ya yi biyayya ga kiran da aka yi masa na yin murabus domin samun daidaito da gaskiya da adalci.
Daily Trust ta ruwaito cewa a lokacin da ake tattaunawa da Lukman a yayin da ake gabatar da wani shiri na AIT a kwanakin baya, ya zargi sakataren jam’iyyar APC na kasa, Sanata Iyiola Omisore, wanda kuma mamba ne a kwamitin gudanarwar jam’iyyar APC da karkatar da kudaden da aka ware domin yakin neman zaben gwamnan Jihar Osun a shekarar da ta gabata da kuma zarginsa da haddasa rikicin. Sai dai APC ta sha kaye a zaben.
Haka kuma ya zargi sakataren jam’iyyar na kasa da kara raba kan jam’iyyar reshen Jihar Osun, ya kuma yi kira da ya yi murabus.
Sai dai a wata wasika da Omisore ya aike wa Lukman ta hannun Lauyansa, Gboyega Oyewole, ya bukaci mataimakin shugaban jam’iyyar da ya janye kalamunsa da aka yi masa a cikin jaridun kasar guda biyu da wasu kafafen yada labarai na yanar gizo da dama, sannan ya biya shi naira miliyan 500 bisa wannan kazafi da ya yi masa da bata sunan cikin sa’o’i 48 ko kuma ya fuskanci shari’a.
Sai dai wani magoyin bayan Lukman ya ki janye maganar, inda ya ce a shirye yake da ya fuskanci Omisore.
“Ina nan kan bakana cewa Omisore ya kasa hada kan shugabannin jam’iyyar APC da ‘ya’yan jam’iyyar a Jihar Osun, wanda shi ne ya jawo muka fadi zabe. Yana adawa da duk wata bukata ta neman a yi masa hisabi, kuma yana daukar matakan tsoratarwa ne domin watakila a yi amfani da tsarin nada mukamai a gwamnatin tarayya da Tinubu zai jagoranta,” in ji shi.
Bayan kammala zabukan 2023, jam’iyya mai mulki ta fada cikin rikice-rikice a jihohi, bisa zargin cin amanan jam’iyya har ta kai ga korar jami’ai da jiga-jigai a wasu jihohi.
An dakatar da wasu daga cikin mambobin kwamitin gudanarwa na jihar, yayin da wasu kuma aka kore su bisa zargin cin zarafin jam’iyya.
Kwamitoci daban-daban da jam’iyyar ta kafa a jihohi sun ba da shawarar daukar matakin ladabtarwa kan wasu jiga-jigai da wasu ‘ya’yan jam’iyyar da ake zargin sun yi wa ‘yan takarar PDP da na LP aiki.
Misali, jam’iyyar APC a Inugu ta ce ta dakatar da Geoffrey Onyeama, ministan harkokin waje da Ken Nnamani, tsohon shugaban majalisar dattawa daga jam’iyyar.
Jam’iyyar ta kuma kori Sulliban Chime, tsohon gwamna da Eugene Odoh, tsohon kakakin majalisar dokokin jiha, Osita Okechukwu, darakta-janar na gidan rediyon Muryar Nijeriya (BON) da dai sauransu, kan wasu zarge-zarge na cin amanan jam’iyyar.
Da yake zantawa da manema labarai bayan taron majalisar zartarwar jam’iyyar, sakataren jam’iyyar APC, Robert Ngwu ya ce ayyukan da suka saba wa jam’iyyar na kawo cikas wajen cika aikinta da kuma cutar da tsarin dimokuradiyya.
Sai dai Okechukwu da wasu sun yi watsi da ikirarin dakatar da su.
Kazalika, jam’iyyar APC reshen Jihar Bauchi ta dakatar da shugabanta, Alhaji Babayo Aliyu Misau, bisa zargin kin zaben dan takarar gwamnan na jam’iyyar APC a zaben gwamnoni da aka kammala.
Ana zargin Misau da aikata wasu abubuwa na kin jinin jam’iyyar kafin zabe da kuma lokacin zabe wanda suka kawo cikas ga nasarar jam’iyyar.
Shi ma tsohuwar mai taimaka wa shugaba Buhari kan harkokin yada labarai kuma shugabar hukumar raya yankin Neja Delta (NDDC), Lauretta Onochie, shugabannin jam’iyyar APC sun dakatar da ita a gundumarta ta Onicha-Olona 4 da ke Jihar Delta.
Wani kudiri na shugabannin unguwannin mai dauke da sa hannun Ogbolu Peter Nduka da Justina Amagor Akaeze (shugaban da sakatariya) tare da wasu mambobin kwamitin 25 na karamar hukumar Aniocha ta Arewa sun tuhume ta da ayyukan cin amanan jam’iyyar APC.
Haka kuma wasu mambobin kwamitin zartarwa na jam’iyyar APC reshen Jihar Ribas sun dakatar da shugabanta, Emeka Beke da Iheanyichukwu Azubuike, bisa zargin cin amanan jam’iyyar a zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu.
Amma Beke ya ce mambobin zartaswa ba su da hurumin dakatar da shi, yana mai zargin cewa hadin kan da jam’iyyar PDP ke ci gaba da samu su suka janyo faduwar APC a jihar.
Ita ma jam’iyyar APC a Jihar Neja ta dakatar da shugabanta, Haliru Zakari Jikantoro bisa zargin cin amanan jam’iyyar a lokacin zabe.
Shugabannin gundumar Kashini na jam’iyyar a karamar hukumar Agwara sun dakatar da Jikantoro, bisa zarginsa da saba kundin tsarin mulkin jam’iyyar da haddasa rikicin gabanin zaben gwamna da na ‘yan majalisar jiha.
Haka kuma, an dakatar da wani jigo a jam’iyyar APC a Jihar Edo, Janar Charles Arhiabbere (mai ritaya), bisa zargin cin zarafin jam’iyyar. An sanar da dakatar da shi ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Felid Ehigiegba da Edward Obiawe (shugaba da kuma sakatare) na Oredo ward 1, da wasu 20 tare da mika wa uwar jam’iyyar.
A bangare daya kuma, har yanzu rikicin PDP ya ki ci ya ki karawa.
Wasu da dama sun yi tunanin rikicin da ya dabaibaye babbar jam’iyyar adawa ta PDP bayan zaben fid da gwanin na takarar shugaban kasa a watan Mayun bara zai zo karshe bayan kayen da jam’iyyar ta sha a zaben, amma hakan bai tabbata ba, domin kuwa rikicin ta kara kamari wanda ya kai ga korar shugaban jam’iyyar na kasa, Dakta Iyorchia Ayu.
Duk da cewa har yanzu magana na gaban kotu, masu ruwa da tsaki na jam’iyyar na ganin cewa Ayu ya riga ya fice kamar yadda aka tilasta masa barin ofishi.
Wasu na gargin an cire Ayu daga mukaminsa ne sakamakon zargin cin hanci da rashawa da sauran batutuwa.
Duk da kasancewarsa gwamnan Jihar Benuwe, Samuel Ortom, amma Ayu bai kubuta daga hannunsa ba yayin da aka mika shi gaban kwamitin ladabtarwa na jam’iyyar ta kasa.
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa dakatarwar ta kasance kusan yanke shawara ne bayan kokarin da wasu mambobin kwamitin gudanarwa na jam’iyyar suka yi na shiga tsakani.
Sai dai Ayu ya dage tare da yin amfani da ikonsa na kin amincewa da dakatarwar.
Ayu ya shiga cikin rikici ne tun lokacin da shugabannin jam’iyyar PDP da ke gundumarsa ta Igyorob a karamar hukumar Gboko na Jihar Binuwai suka yanke shawarar dakatar da shi kan batutuwan da suka shafi gudanar da zaben da ya gabata.
Da yake jawabi ga taron manema labarai kan lamarin, Mista Bangeryina Dooyum, sakatariyar gundumar Igyorob, wanda yake shugabantan jam’iyyar ya ce, “Mun lura matuka cewa Dakta Iyorchia Ayu, wanda shi ne shugaban jam’iyyar PDP na kasa ya yi kokarin hana jam’iyyar samun nasara a gundumar Igyorob.”
Dakatarwar ta biyo bayan matakin kotu na hana Ayu ya kira kansa a matsayin shugaban jam’iyyar PDP.
Duk da irin bajintar da ta nuna a zabukan da aka kammala na shekarar 2023, shugabancin jam’iyyar LP ya fada cikin rikici da ke raba jam’iyyar da kara samun tagomashi.
Dakatarwar da wata babbar kotun tarayya da ke Abuja hana Julius Abure gabatar da kansa a matsayin shugaban jam’iyyar LP na kasa ya kara rura wutar rikici a cikin jam’iyyar.
An dai dakatar da shi ne tare da jami’ai uku bisa zargin aikata laifin bayar da jabun bayanai.
Alkalin kotun, Mai shari’a Hamza Mu’azu, ya kuma bayar da umarnin a bai wa jami’an da aka dakatar tsarin yadda kotun ta fara aiki, manyan jami’an da aka takatar sun hada da Abure, sakataren jam’iyyar na kasa, Umar Farouk Ibrahim; ma’ajin jam’iyyar na kasa, Oluchi Opara, da kuma sakataren tsare-tsare na kasa, Clement Ojukwu.
Alkalin kotun ya bayyana cewa tsohon dan takarar na neman wani hukumci na wucin gadi ga jami’an hudu da fusatattun ‘ya’yan jam’iyyar su gurfana a gaban kotu da kuma ya amince da hakan.
A wani taron manema labarai, shugaban gunduma na jam’iyyar, Martins Osigbemhe, ya ce hukumar zartaswa ta dakatar da Abure har sai an yanke hukunci kan dimbin koke-koke da kararrakin da ake yi masa a gaban kotu.
Amma sakataren jam’iyyar na kasa, Mallam Farouk Umar, ya yi watsi da dakatarwar, yana mai bayyana hakan a matsayin haramtacce.
Ya ce kundin tsarin mulkin jam’iyyar ya bayyana karara yadda za a iya dakatar da shugabanta na kasa.
Sai dai kuma a wannan rana, yayin da kotun Abuja ta umarci Abure da ya daina bayyana kansa a matsayin shugaban jam’iyyar na kasa tare da wasu mutane uku, wata babbar kotu a birnin Benin, babban birnin Jihar Edo, ta hana jam’iyyar aiwatar da dakatar da shugaban jam’iyyar na kasa, Julius Abure har zuwa lokacin da za a yanke hukunci kan lamarin.
Rikicin dai ya kai ga nuna karfin tuwo da sansanoni biyu da ke adawa da juna, lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ce a lokacin da wasu jiga-jigan jam’iyyar na jihohi suka fatattaki bangaren Lamidi Apapa na kwamitin ayyuka na kasa daga hedikwatar jam’iyyar ta kasa da ke Abuja.
A ranar Juma’ar da ta gabata, shugabannin jam’iyyar sama da 30 ne suka shiga hedikwatar jam’iyyar, inda suka dage cewa Abure shi ne shugabansu.
Sai dai da yake zantawa da manema labarai a ranar Laraba a kofar ofishinsa, shugaban jam’iyyar LP na Jihar Kwara, Cif Kehinde Rotimi, ya ce shi da takwarorinsa sun je taron ne amma an kulle su a wajen sakatariyar wanda shugabannin jihohi suka ki ba su izinin shiga, wanda hakan ya tilastawa kowa ya tsaya a waje.
Da yake mayar da martani kan lamarin, tsohon shugaban matasa na LP, Anslem Eragbe, wanda kwamitin gudanarwa na jam’iyyar ya dakatar, ya ce suna yin aiki ne kawai da kundin tsarin mulkin jam’iyyar, inda ya koka da yadda shugabannin jihar ke yi wa shugaban riko na kasa zagon kasa.
A bangaren jam’iyyar NNPP kuwa, Tsohon shugaban jam’iyyar NNPP na kasa, Farfesa Rufa’i Alkali, ya yi murabus a karshen watan Maris, makonni biyu kacal bayan zaben gwamnan da jam’iyyar ta lashe Jihar Kano.
Ko da yake akwai jita-jitar cewa rikici ne ya tilasta wa Alkali ya yi murabus, amma shugabannin jam’iyyar sun dage cewa matakin da ya dauka yana da kyau.
Shugaban riko na jam’iyyar, Alhaji Abba Kawu Ali, a lokacin da yake zantawa da manema labarai kwanan nan a Abuja, ya gode wa Farfesa Alkali bisa yadda ya kula da nasarar da jam’iyyar ta samu a zaben gwamna, inda ya ce, “Ba za mu manta da shi ba saboda gudunmawar da ya bayar, domin babu wanda zai kwace masa wannan.”
Ya dage kan cewa babu wani boyayyen dalili na murabus din Alkali, yana mai cewa ya koma gefe ne domin bai wa matasan Nijeriya damar karbar shugabancin jam’iyyar tare da ciyar da ita gaba.
Wata majiya a jam’iyyar ta bayyana cewa murabun din Alkali yana da nasaba da babban zabukan da aka gudanar.
Majiyar wadda ta ki yin karin haske kan batun, ta ce jam’iyyar ba ta cimma burinta ba a zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya na ranar 25 ga watan Fabrairu, da na gwamnoni da na majalisun jihohi da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris.
Wasikar da Alkali ya sanya wa hannu kuma ya aika wa sakataren jam’iyyar na kasa, Dipo Olayeoku, ta ce, “Na ji dadin rubutawa da kuma isar muku cewa na ajiye mukamin shugaban jam’iyyar NNPP daga ranar 31 na watan Nuwamban 2023.
Dalilan Da Ya Sa Jam’iyyu Ke Fadawa Rikicin Cikin Gida – Manazantar Siyasa
A nasa jawabin daraktan makarantar nazarin Zamantakewa da harkokin siyasa ta Abuja, Dakta Sam Amadi, ya ce rikice-rikicen da ke kunno kai a manyan jam’iyyun siyasa alama ce ta dimokuradiyyar Nijeriya, inda ya kara da cewa mutane da dama ba su fahimci tsarin dimokuradiyya ba.
Ya ce, “An kafa tsarin siyasarmu ne kan turbar ta’addanci. Kamar ‘yan fashi, sun dogara da karfin makamin da suke da shi. ’Yan fashi ’yan kasuwa ne, suna fashi ne domin samun kayayyaki. Kamar ‘yan fashi, ‘yan siyasarmu na amfani da tashin hankali a wasu lokutan don kawo cikas ga harkokin siyasa.
“Akwai hanyoyin da ake bi wajen zaben mutane, amma yin amfani da tsarin ‘yan fashi ba zai harfar da da mai ido ba, da gangan suke karya doka don tsige mutane daga mukamansu. Ba su fahimci cewa doka ta tilasta musu ba.”
Sai dai ya ce mafita ita ce sanin cewa dimokuradiyya ba wai ta ta’allaka ga zabe ne kadai ba, har da yadda za a kafa tsarin doka.
Shi ma da yake nasa jawabin, malami a jami’ar Abuja, Farfesa Kari Abubakar Umar, ya lissafo dalilan da suka haddasa rigingimun a manyan jam’iyyun siyasa Nijeriya bayan zaben.
Kari, a wata tattaunawa ta wayar tarho, ya ce abubuwan da ke haddasa rikici a manyan jam’iyyu sun hada da cin amanan jam’iyya da kuma rashin nasrar jam’iyya da dai sauransu na haifar da rikicin bayan zabe a jam’iyyun siyasan Nijeriya.
Ya ce, “Daya daga cikin manyan abubuwan da jam’iyyun siyasa ke da shi a wannan jamhuriya shi ne, rikicin cikin gida da ba ya karewa. Jam’iyyun dai na da mabambamtan rikice-rikice masu tsanani tun da farko, watakila saboda galibin su idan ba duka ba, ‘yan siyasa da ke cikin karkashin inuwar jam’iyya ba su da alkibla guda daya.
“A kowani lokaci ‘yan siyasa suna kokarin cimma ra’ayinsu. Suna son amfani da jam’iyyar a matsayi wani dandalin, shi ya sa kowane karamin al’amari yakan haifar da rikici a tsakaninsu.
“Akwai wasu lokuta na musamman da jam’iyyun siyasa ke fama da rikice-rikice, kuma sakamakon zaben na daya daga cikinsu. Sauran lokutan sun hada da lokacin da aka zabi jami’an jam’iyya, lokacin zaben fid da gwani, sannan akwai dalilai da yawa a kan hakan.
“Ayyukan cin amanan jam’iyya na iya kasancewa daya daga cikin babban sila na fadawar manyan jam’iyyu cikin rikicin bayan zabe ta yadda mutane suka gudanar da kansu tun daga farko har zuwa karshen zaben. Mafiyawancin lokuta idan aka kammala zabe ana iya samun rikicin cikin gida na jam’iyyu.
“Har ila yau, akwai batun yadda jam’iyyar ta yi rashin nasara da kuma rashin jin dadin ‘ya’yan jam’iyyar. Don haka, ko da yaushe za su sa wasu su yi wa wasu zagon kasa.
“Wani babban al’amari kuma shi ne, yawancin sakamakon zabe yana ba da damammaki daban-daban da ke haddasa rarrabuwar kawuna a tsakanin ‘ya’yan jam’iyya da son yin mulki, kamar abin da ke faruwa a PDP a yanzu. Mabambantan ra’ayoyi na sha’awar karbir ragamar jam’iyyar da kuma samun mukamai domin ci gaban siyasarsu.
“A jam’iyyar APC, ana zargin wasu mutane da yi wa jam’iyya zagon kasa da kuma ayyukan cin hanci da rashawa, don haka a al’adance, dole a nemi mutanen da za su daidaita lamura,” in ji Kari.