Daga Muhammad Maitela,
A taron farfado da hadin kan matasan jam’iyyar PDP a Gashuwa, shalkwatar karamar hukumar Bade da ke Jihar Yobe ya jawo cece-ku-ce tare da daga hankalin jiga-jigan jam’iyyar APC mai mulki. Yayin da wasu matasan suka fice zuwa PDP tare da bayyana dalilin daukar matakin da cewa sun yi hakan ne zargin an yi watsi da su a jihar.
Wannan al’amarin ya gudana ne a wani taron karbar matasan a babban dakin taro da ke Gashuwa a karshen mako.
Daruruwan matasa suka halarci taron daga kananan hukumomin Yusufari, Nguru Karasuwa, Jakusko, Potiskum tare da samun wakilcin manyan jiga-jigan jam’iyyar PDP a Jihar Yobe irin su tsohon ministan ma’aikatar kula da harkokin ‘yan sanda, Alhaji Adamu Maina Waziri, tsohon dan takarar gwamna a jihar Yobe, Ambasada Iliya Damagum, tsohon dan takarar kujerar sanata a shiyyar gabashin Jihar Yobe, Hon. Abba Gana Tata da makamantan su.
A nasa bangaren, jami’in yada labarai na matasan jam’iyyar PDP a Inwar Lamar, Abubakar Sadik Abdullahi ya bukaci matasa a jihar da cewa lokaci ya yi wanda za su cire tsoro, su fito don kwatar yancinsu. Ya kara da cewa idan a baya an danne hakkokinsu, to yanzu jam’iyyar PDP ta share musu hawaye ta hanyar ba su cikikkiyar damar domin a dama da su a harkokin siyasa.
Sadik ya kara da cewa, matasa a Jihar Yobe a karkashin jam’iyyar PDP sun shirya tunkarar zabukan 2023 wajen ganin sun kwace mulki daga hannun APC tare da bayar da tabbacin samun goyon bayan jama’a.
Ita ma shugabar matan jam’iyyar PDP a karamar hukumar Bade, Fatima Muhammad Umar, ta bayyana cewa sun dauki dogon lokaci suna kokari wajen hada kan ‘ya’yan jam’iyyar don fuskantar alkibla daya tare da kauce wa abubuwan da za su kawo baraka da rabuwar kai a PDP.
Ta ce tunanin hakan ya zo ne biyo bayan la’akari da jiga-jigan jam’iyyar suka yi bisa wasu matsaloli da bambance-bambancen da aka sha fama da su a baya, wadanda suka kasance tarnaki a PDP, yayin da suka bayar da shawarar kirkiro da wani bangaren matasa maza da mata tare da sanya masa suna da: Inwar Lamar Matasan PDP, wanda ake sa ran zai shiga fadin jihohin kasar nan.
A nasa jawabinsa, shugaban matasan PDP a karamar hukumar Bade, Hon. Abdullahi Buba Katuzu, ya bayyana cewa matasa ne ‘yan gani-kashenin PDP suka shirya wannan taron domin hada kansu a yi tafiya mai tsabta a jam’iyyar. Ya ce wannan yana da nasaba da adalci da kulawa ta musamman da PDP ta bai wa matasa.
Da yake zantawa da manema labarai jim kadan da kammala taron, Hon. Shariff Abdullahi, wanda ya wakilci Ambasada Iliya Damagum, ya ce, “Mun taru ne a wannan waje domin karfafa matasan jam’iyyar PDP.”