Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba sun kai farmaki kauyen Kubat da ke karamar hukumar Mangu ta Jihar Filato a safiyar ranar Talata, inda suka kashe wasu mutanen kauyen.
Wata majiya daga al’ummar yankin ta ce mutane da dama ne suka mutu a lokacin da ‘yan bindigar suka afka wa al’ummar da sanyin safiyar, inda suka bude wuta kan jama’a lamarin da ya haifar da rudani.
- Wani Mutum Ya Kashe Kishiyar Mahaifiyarsa A Kogi
- Bai Kamata A Ba Emefiele Hutun Zuwa Karo Karatu Ba –Matawalle
Ya kuma kara da cewa wasu mutane da dama sun samu raunuka daban-daban.
A halin da ake ciki, gwamnan Jihar Filato, Simon Lalong, wanda ya tabbatar da harin da kashe-kashen a wata sanarwa mai dauke da sa hannun daraktan yada labaransa, Dokta Makut Simon Macham, ya ce ya farka da safiyar Talatar nan da wani labari mai ban tausayi, harin da aka kai kauyen Kubat da ke karamar hukumar Mangu inda aka ce an kashe wasu mutane da suka hada da mata da yara.
A cewar sanarwar, Lalong ya damu matuka game da wannan lamari mai cike da bakin ciki, kuma nan take ya umarci jami’an tsaro da su binciki lamarin tare da tabbatar da kama masu hannu a ciki.
Lalong ya bayyana harin a matsayin wani yunkuri na masu aikata laifuka na mayar da jihar cikin duhun kwanakin da aka wuce, ya shan alwashin cewa gwamnati ba za ta sa kafar wanda daya da duk wanda ya shiga hannu.
Yayin da yake yin Allah wadai da wannan aika-aika, gwamnan ya jajanta wa wadanda abin ya shafa, ya kuma ba da tabbacin cewa ba za a bar wadanda suka yi kisan ba a hukunta su ba.
Sanarwar ta kara da cewa, gwamnan ya kuma umarci hukumar bada agajin gaggawa ta jihar da hukumar samar da zaman lafiya da su kai ziyara yankin tare da tabbatar da bukatun jin kai domin kai dauki ga wadanda abin ya shafa yayin da ake gudanar da cikakken bincike.