Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun sace mutane biyar, ciki har da jariri ɗan wata ɗaya da haihuwa, a Mararaban Kajuru, ƙaramar hukumar Kajuru ta Jihar Kaduna.
Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 1 na daren ranar Talata, 20 ga watan Oktoba, 2026, a unguwar Kufana.
Wani saƙo da ya shafi tsaro, ya tabbatar da faruwar lamarin tare da kira ga jama’a da su yi addu’ar ceto waɗanda aka sace cikin ƙoshin lafiya.
Sai dai, saƙon bai bayyana sunayen waɗanda aka sace ba, kuma bai yi ƙarin bayani kan yadda aka sace su ba.
Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, rundunar ’yansandan Jihar Kaduna da Ma’aikatar Tsaron Cikin Gida ta jihar ba su fitar da sanarwa a hukumance kan lamarin ba.














